Akalla mutane uku ne jami’an rundunar tsaro ta civil Defence reshen jihar Gombe, suka kama da laifin barnata kadarori na kamfanin jiragen kasa na Najeriya.
An gabatar da su ne tare da wani wanda aka ce ya kasance mai garkuwa da mutane a jihar.
Da yake jawabi yau Talata yayin ganawa da manema labarai a rundunar, Kwamandan rundunar Waziri Goni, ya ce kayayyakin da aka lalata sun hada da mashinfidin jirgin kasa, da sauran wasu muhimman kayayyaki.
A cewarsa, mutanensa sun tunkari barayin bisa ga rahoton leken asiri, inda ya kara da cewa goyon bayan al’umma ya taimaka wa wannan nasara.
Ya ce, “’Yan ukun mabarnata ne kuma suna lalata layin dogo daga Gombe zuwa Bauchi da kuma daga Bauchi zuwa Nafada.
Ya bayyana cewa ana ci gaba da gudanar da bincike domin bankado masu sayan kayan an sata, da kuma sauran kungiyoyin da ke da alaka da wannan danyen aikin.
Har ila yau, an kama wani matashi mai shekaru 30 da haihuwa wanda ya yi garkuwa da shi.
Goni ya bayyana cewa mutanen nasa suna kan hanyar sa ta zuwa wajen barnar lokacin da aka kama shi.