Duk wanda yayi Kalaman Ɓatanci Ga Annabi Isah zai gamu da fushin Allah — Fasto Adebayo
Shugaban Cocin Redeemed Christian Church of God, Fasto E. A Adebayo ya gargaɗi mutane akan cewa duk wanda yayi Kalaman Ɓatanci Ga Annabi Isah zai gamu da fushin Allah.
KARANTA WANNAN LABARIN: INEC ta koka kan ƙarancin masu rajistar Katin Zaɓe a Jahar Katsina
Adebayo wanda yayi wannan jawabin a taron Cocin RCCG na wata-wata na wata Juli, Wanda ya gudana a yammacin Juma’a da kuma safiyar ranar Asabar, yayi wannan jawabin ne akan hare-hare da Kashe-kashe da ake kaiwa Coci da masu ibada a sassan Ƙasar.
Majiyar Jaridar Dimokuraɗiyya ta ruwaito cewar kimanin masu ibada ƴan cocin Katolika 40 ƴan bindiga suka hallaka a watan Yuni a cocin St. Francis Catholic Church dake Owo, Jihar Ondo.
Makonni biyu bayan kai hari a Owo, ƴan bindiga sun sake hallaka mutane uku a wasu hare-hare a Cocin Baptist, da St. Moses a Ƙaramar Hukumar Kajuru ta Jihar Kaduna.