Daga: Abbas Yakubu Yaura
Rundunar sojin ruwan Najeriya ta bayyana cewa, ana ci gaba da kokarin ganin an ceto daya daga cikin ma’aikatanta mai suna Able Seaman Musa Lawal wanda ake zargi an yi garkuwa da shi a Unguwar Wada Post Flood da ke Lokoja a Jihar Kogi.
Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa kudin fansar da aka yanke za’a biya na Naira miliyan 3 da aka nema domin a sako ma’aikacin, an yi shawarwarin an rageshi zuwa kasa da Naira miliyan daya.
KARANTA WANNAN LABARIN: https://dimokuradiyya.com.ng/ina-tare-da-buhari-duk-da-rashin-adalcin-da-aka-yiwa-tinubu-amosun-ya-koma-jamiyyar-apc/
Daraktan Yada Labarai na Sojojin Ruwa, Commodore AO Ayo-Vaughan wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya bayyana cewa an yi garkuwa da Able Seaman ne a gidansa na kashin kansa da ke unguwar Wada Post Flood Housing Estate, a Ajaokuta ta Jihar Kogi da sanyin safiyar Talata.
“Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba suka shiga gidansa da karfi suka yi awon gaba da shi. Daga nan ne suka tuntubi iyalan suka bukaci a biya su kudin fansa naira miliyan uku. Uwargidan wanda aka sace tana rokon su kuma sun rage kudin fansa zuwa Naira miliyan daya,” inji shi.
Kakakin Rundunar Sojin Ruwa ya bayyana cewa, Able Seaman Lawal ma’aikaci ne da ke aiki a reshen Gudanarwa a hedkwatar sojojin ruwa yana mai nuni da cewa yana hutun hukuma kafin lamarin ya faru.
Bugu da kari, Commodore Vaughan ya ce sansanin sojojin ruwa na Najeriya, NNS Luggard yana aiki tare da ‘yan sandan Najeriya a Lokoja don tabbatar da ceton jami’in.
Sai dai JARIDAR DIMOKURADIYYA ta tattaro cewa babban jami’in , an ce yana gudanar da rayuwa mai kyau a cikin al’umma kuma yana haba haba da mutane da dama, har ya kai ga yin taho-mu-gama da wasu mutanen al’ummar.
Wannan ya saba wa nasiha daga hukumomin sojojin ruwa wadanda a lokuta da dama su kan yi gargadi ga jami’an da ba sa zama a barikin da su kula da halayensu da alakar su, musamman a wannan lokaci na rashin tsaro da sauran kalubalen da ke fuskantar al’umma.