ISWAP tace ita keda alhakin kai harin Kuje, ta saki bidiyo
Ƙungiyar Ƴan Ta’addan ISWAP tace ita keda alhakin kai harin gidan yarin Kuje inda aka saki Fursunonin wurin a Abuja.
Ƴan Ta’adda sun bayyana alhakin kai harin a cikin wani bidiyo da suka saki a daren ranar Laraba.
KARANTA WANNAN LABARIN: Abokin Takara: Wasu Jiga-Jigai a APC, sun buƙaci Kotu ta hana Tinubu canja Kabir Masari
A cikin bidiyon, ƴan Ta’addan sun nuna yadda wasu daga cikin mambobin suka shiga gidan yarin Kuje.
Bidiyo mai daƙiƙa 38 ya nuna yadda ƴan ta’adda suka yi ta Harbe-Harbe kafin su samu damar shiga gidan yarin.
A dubawar da Majiyar mu tayi, ya nuna yadda ƙungiyar ta fara sakin bidiyon da larabci mai taken “Mayaƙan ISWAP sun kai hari a gidan yarin Kuje a jiya, kuma sun samu nasarar sakin fursunoni da yawa.”
Bidiyon ya nuna yadda Dattijai suke ta magana, inda suke bayyana ɗaukar alhakin kai harin da ƙona wurin.
Hukumar kula da Gidajen Gyaran Aƙidu na Ƙasa sun nuna cewa Fursunoni huɗu sun hallaka, a yayinda guda 879 suka tsere a lokacin kai harin.
Jami’in Hulda da jama’a na Hukumar Mr Abubakar Umar a cikin sanarwar daya fitar yace maharan sun karya katangar gidan yarin, ta hanyar amfani da bam.
Ya kuma tabbatar cewa Mataimakin Kwamishinan Ƴan Sanda Abba Kyari, da sauran manyan mutane basu tsere daga gidan yarin ba.