An yi garkuwa da limamin Katolika na Kaduna, Very Rev. Fr. Yayin da yan bindigan suka kashe John Mark Chietnum, da su ke rike dashi a hannun su.
Wani limamin coci, Rev. Fr. Donatus Cleopas, wanda aka yi garkuwa da shi, ya tsere daga hannun masu garkuwar.
An yi garkuwa da su ne a ranar 15 ga watan Yuli a cocin Rector of Christ the King Parish da ke Yadin Garu a karamar hukumar Lere a jihar Kaduna.
Wata sanarwa da cocin Katolika na Kafanchan, Rev.Fr Emmanuel Uchechukwu Okolo, ya fitar, ta ce an gano gawar Rabaran Chietnum a ranar Talata.
An ce an kashe shi ne a ranar da aka sace su.
Har zuwa rasuwarsa, Rev Chietnum shi ne shugaban CAN na karamar hukumar Jema’a kuma shugaban CAN na Kudancin Kaduna.
A halin da ake ciki wasu ‘yan bindiga sun kashe wasu mutane biyar a kauyen Ganin-Gari da ke unguwar Randagi a yammacin karamar hukumar Birnin Gwari a jihar Kaduna.
Wata sanarwa dauke da sa hannun shugaban kungiyar masu son ci gaba a masarautar Birnin-Gwari (BEPU), Ishaq Usman Kafai, ta ce an kai harin ne a ranar Lahadin da ta gabata, yayin da ‘yan bindigar da yawansu ya kai 40 a kan babura suka far wa al’umma yankin .
Ya ce barayin sun kashe mutane biyu, sun yi awon gaba da shanu tare da yin garkuwa da wasu mutanen da ba a tantance adadinsu ba.
Kafai ya ce rundunar hadin guiwa ta ‘yan sanda da ‘yan banga na yankin sun yi artabu da ‘yan bindigar a kewayen gadar Tudun Wada tare da kubutar da duk wadanda aka yi garkuwa da su da kuma shanun da aka sace.
“A kan hanyarsu ta komawa maboyar su, (’yan bindiga) sun kashe wani mahaukacin yaro wanda suka ci karo da shi a kan hanyar unguwar Dawakin Bassa.
“A ranar Litinin kuma sun kashe wasu mutane biyu a gonakinsu wanda ya kawo yanzu adadin mutanen yankin da aka kashe ya kai biyar,” inji shi.