Abokin Takarar Obi, Ahmed Datti ya caccaki Buhari kan rashin tsaro, yace ba abinda zai iya yi har ya sauka
Yusuf Ahmed-Baba, Mataimakin Dan Takarar Shugaban Ƙasa na jam’iyyar Labour, LP, a ranar Litinin ya zargi Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari da gazawa wajen magance matsalar rashin tsaro a ƙasar.
Ahmed-Baba ya ce ya ji kunya cewa Buhari ya gaza wajen tabbatar da tsaro a Najeriya duk da maganar da ya yi na magance matsalar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ƴan Sanda sun Cafke Fitaccen Lauya Kan Takardun Bogi
Ya yi magana ne a gidan Talabijin na Channels a Shirin Siyasar mu a yau, yayin da yake mayar da martani kan yadda Ɗan tatkarar Shugaban Ƙasa na LP, Peter Obi ke da niyyar magance rashin tsaro.
Ahmed-Baba ya tabbatar wa ƴan Najeriya kiyaye lafiyar su idan Obi ya lashe zaɓen Shugaban Ƙasa a 2023.
Ya ce: “Muna yi, minen ƴan Najeriya ba su ji ba a baya? Me APC bata faɗawa Yan Najeriya ba? Me Buhari bai ce ba game da dawo da tsaro? Shin ’yan Najeriya ba su gaji da jin magana da yin akasin haka ba?
“Ni da Peter Obi ba mu da bambanci, shi ya sa muke neman wannan damar kuma idan muka samu za mu isar da shi.
“ Gwamnatin nan ta lalata komai, ina jin kunyar yin magana saboda wani kamar Buhari ya yi magana ya kasa.
“Ba na son yin magana sai dai mu yi aiki, muna da mafita kuma da yardar Allah ‘yan Najeriya za su kasance cikin koshin lafiya.