Jami’an tsaron ‘yan Sandan Nijeriya sun saki wakilin Babban gidan Talabijin na PRESS TV bayan kama shi da suka yi yayin da yake kokarin daukar rahoton masu muzaharar neman ganin an saki jagoran Harkar Musulunci, Shaikh Ibraheem Zakzaky wanda almajiransa suka gudanar a Sakateriya dake birnin tarayya Abuja.
Sakin Danjuma Abdullahi ya biyo bayan kiran da Kwamishinan ‘yan sandan ya yi ma ofishin dake tsare da shi.
Majiyarmu ta tabbatar mana da cewa bayan ‘yan sandan sun saki Danjuma Abdullahi da Innocent Michael, sun mika su ne gad an jaridar kafar watsa labaran Faransa ta RFI, Mohammed Sani wanda ya tsayawa ‘yan jaridar kafin Kwamishinan ‘yan sanda, Bala Ciroma ya sanya baki a sake shi.
Bayan fitowarsa, Danjuma Abdullahi ya tabbatar da cewa bai fuskanci wani hujumi da musgunawa a wurin ‘yan sandan ba. Inda ya mika godiyarsa ga Kwamishinan ‘yan sandan kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Facebook.
An kama Danjuma Abdullahi ne tare da ‘camera man’ dinsa bayan kammala muzaharar da aka gudanar na tunawa da “kisan” da da ‘yan Sanda suka yi wa ‘yan shi’a a shekarar da ya gabata a Abuja.