Shahararren ɗan wasan nan ɗan asalin ƙasar Turkey wanda ya koma ƙasar Jamus da zama wato Mesut Ozil ya ajiye wani babban tarihi da ba kowanne ɗan wasa ne zai iya ajiyeshi ba a duniyar ƙwallon ƙafa.
Wannan tarihi da Ozil ya ajiye ba a taɓa samun wani ɗan wasa da ya ajiye irinsa ba a gasa daban-daban da Ozil ya buga a tarihin fafata wasan ƙwallon ƙafarsa da yayi kama daga ƙasarsa da kuma dukkanin ƙungiyoyin da ya bugawa wasanni.
Ga tarihin da ya ajiye kamar haka:
Ozil ne ɗanwasa tilo a duniyar ƙwallon ƙafa da yafi taimakawa wajen jefa ƙwallaye idan aka hade dukkanin wasannin daya buga a jerin gasoshi kamar haka.
1. Gasar ajin Firimiya ta ƙasar Ingila.
2. Gaaar Bundes Liga ta ƙasar Jamus.
3. Gasar Laliga ta ƙasar Andalus.
4 gasar ajin ƙwararru ta nahiyar turai wato Europa League.
5. Gasa zakarun nahiyar turai wato Uefa Champions League.
6. Gasar da akeyi ta nahiyar turai wati Euro Cup.
7. Da kuma gaaar cin kofin duniya da bature yame kiransa da World Cup.