Ƴan Najeriya sun fara tattaki a Ƙafa, a yayinda Man Fetur yayi karanci a Babban Birnin Tarayya Abuja.
Majiyar Jaridar Dimokuraɗiyya ta ruwaito yadda Shugaban Ƙungiyar Kula da Man Fetur Mr Farouk Ahmed ya bada tabbacin shigowa da Man Fetur mai yawa, biyo bayan shigowa da Gurɓataccen man fetur ga Al’umma.
Wannan ba shine matsalar ba, domin ƙarancin man fetur a Abuja ya tsananta.
KARANTA WANNAN LABARIN: Zaben FCT: Zababben Shugaban AMAC Ya Yabawa Buhari, INEC, Tare Da Son A Yi Wa Dokar Zabe Kwaskwarima
A yayin da Majiyar mu ta zagaya a Babban Birnin Tarayya Abuja, Ma’aikata suna a tsai-tsaye a wurin jiran Mota, inda Motoci kadan ne ke akan hanya.
Da yawan mutane, tuni sun fara tattaki domin zuwa inda suka dosa, ganin cewa da yawa daga cikin Motocin haya suna wajen shan Mai domin jiran a zuba masu.
A wasu wuraren cikin Abuja, ana saida Man Fetur ta kasuwar bayan fage akan Naira ɗari 400 ko 1000.
Matsalar Man Fetur ya kuma haddasa karuwar kuɗin Man fetur, inda ya linka sau biyu a dukkanin garin.
Dayake magana da wakilin Majiyar mu, wani Ma’aikaci mai suna Joshua yace “bansan mi gwamnati mi take yi ba, domin gidajen man fetur abun yayi tsanani.