Ƙungiyar Miyetti Allah Tayi Amai Ta Lashe Kan Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa Da Ta Zaɓa
Kungiyar Makiyaya ta Miyetti Allah Cattle Breeders Association of Nigeria (MACBAN) ta ce ba ta amince da wani dan takarar shugaban kasa ko jam’iyyar siyasa ba a zaben 2023 mai gabatowa.
Shugaban kungiyar ta MACBAN na kasa, Alhaji Baba Usman-Ngelzarma ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a ranar Juma’a a Abuja, ya kuma kara da cewa dukkanin manyan jam’iyyun siyasa ba su sanya kalubalen da makiyayan Najeriya ke fuskanta a cikin shirinsu ba, idan sun ci zaɓe.
KARANTA WANNAN LABARIN: Kada Ku Bata Kuri’un Ku, LP Ba Za Ta Je Ko’ina Ba – Okowa Ya Gaya wa Magoya Bayan Obi
Ya ce, “Dole ne in yi bayani domin akwai kungiyoyin Miyetti Allah guda biyu. Muna da kungiyar Miyetti Allah Kautal Hore da kuma Miyetti Allah Cattle Breeders Association of Nigeria (MACBAN), wacce nake wakilta a matsayin shugaban ta na kasa
“A game da kungiya ta Miyetti Allah Cattle Breeders Association of Nigeria, ba mu amince da wani dan takarar shugaban kasa ba.
“Har yanzu muna jiran dukkan ‘yan takarar shugaban kasa su amsa tambayoyinmu kan bukatu bakwai da muka gabatar.
“Har yanzu dai ba mu samu izini daga wani dan takarar shugaban kasa ba. Don haka, har sai lokacin da muka karɓi ɗaya kafin mu fara bincika kuma mu yi la’akari da shi cikin ɗan gajeren lokacin da muke da shi kuma mu yanke shawarar ko za mu iya amincewa da wani ko a’a.
“Don haka kafin mu yanke shawarar wane dan takarar shugaban kasa ne za mu mara wa baya, sai mun zauna tare, mu yi nazari, mu tattauna da ƴan majalisa, domin wannan shi ne bambancin mu da sauran kungiyoyin makiyaya.
“Kuma duk dan takarar da muka amince da shi ne zai lashe zaben saboda muna da masu zabe kusan miliyan 16 daga al’ummar makiyaya a Najeriya.”
Ya yi nuni da cewa ya bi ta kan ka’idoji da tsarin ‘yan takarar shugaban kasa amma bai ga wani abu da ya shafi kiwo ba.
A wani labarin kuma:2023: PDP za ta yi maganin Wike da wasu idan Ɗan takarar su ya bayyana – Tambuwal
Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Tambuwal ya ce jam’iyyar PDP na da hanyoyin da za ta bi wajen tunkarar mambobin da suka yi kuskure.
An bayyana hakan ne a wata sanarwa dauke da sa hannun mai baiwa Tambuwal shawara kan harkokin yada labarai, Muhammad Bello, ranar Juma’a.