Babban malamin addinin musulunci, Sheikh Ahmed Mahmoud Gumi ya bayyana yadda haduwarsa da ƴan bindiga ta kasance a jihar Zamfara.
Jaridar Daily Trust ta Najeriya ta ruwaito cewa Malamin ya damu matuƙa da yadda rashin tsaro ya yi yawa a yankin arewa maso gabashin Najeriya, shi ya sa ya yi tattaki ya tafi har sansanoninsu.
Jaridar ta bayyana cewa Malamin ya shaida wa Gwama Bello Matawalle na jihar Zamfara ranar Alhamis cewa ƴan bindigar sun rikiɗa sun zama ƴan ta’adda saboda wulƙancin da al’umar jihar suke masu.
Ya bukaci gwamnati a dukkan matakai ta yi sulhu da ƴan bindigar, inda ya je tattaunawa ce kawai hanyar da za ta kawo ƙarshen matsalar.
“A mafi yawan sansanonin ƴan bindigar da Fulani da muka shiga, na fahimci babu wani abu da ke faruwa a jihar nan illa ta’ddanci.”
“Wasu na ganin kamata ya yi a yaƙi ƴan bindigar nan sannan a kashe su, amma mu abin da muka fahimta shi ne mafi yawansu ba su da ilimi. Suna bukatar a ilimantar da su sannan a wayar masu da kai,” a cewarsa.
Daily Trust ta ce Gumi ya ce mafi yawan ƴan bindigar sun zama marasa imani ne saboda yawan kai masu hari da mayaƙan sa kai ke kai masu a jihar.