“Ƴan Matan Mijina 87 ne a lokacin da na haɗu da shi” Ƴar Gwagwarmaya
Wata ƴar gwagwarmaya a Najeriya Mrs Adetoun da ace Mijina yana da abokai mata 87 lokacin da na hadu da shi.
Wata mai fafutukar kare haƙƙin bil’adama Adetoun Onajobi ta bayyana cewa Mijinta yana da abokai mata 87 a lokacin da ta hadu da shi.
A wata hira da tayi kwanan nan a tashar WithChude, Adetoun ta bayyana cewa wasu daga cikin matan sun yi duk abin da za su iya yi don ganin sun lalata auren ta.
Ta bayyana cewa ɗaya daga cikin matan 87 budurwa ce ƴar ƙwalisa, mai tsafta” wacce sau da yawa ta kan yi mashi duk abinda yake buƙata.
Mai fafutukar ta bayyana cewa domin ta kawo ƙarshen lagon matan na lalata mijinta da kuma ceto aurenta, sai da ta shiga wasu ƴan dubaru masu alaka da zahiri da kuma ruhaniya.
KARANTA NAN:TSARO: Gwamnatin Najeriya za ta ƙulla Alaƙa da Faransa domin magance tsaro
“Miji na yana da abokai mata 87 da yake ma’amala da su,” in ji ta
Daga cikin ’Yan matan da yake ma’amalar da su, akwai wata da ake kira da Baba Ashabi, har faɗa min take cewa zata bani mamaki, wai zata nema min aiki, shine nace “Ku da ba ku da aikin yi, ina ku ka ga ɗaukar ma’aikata? Ku ma nema ku ke.
Don haka idan mutane suka ce min maza ba za su iya canzawa ba daga yaudara, sai na ce musu ba ku fuskanci yanayi irin na Mijina ba, na dauki matakin Ruhaniya ne, domin akwai waɗanda idan suka neme shi ba ƙaramin aiki bane ya kauce musu, irin su Baba Ashabi.
Akwai wata rana da ya kamata su yi tafiya tare, sai Baba Ashabi ya roki matar cewa ba zai tafi tare da ita ba, amma zai zo ya gana da mahaifiyarsa ne domin ya roke ta.
“A takaice dai, daya bayan daya na yake su, wasu sun zo da daukar fansa a wurin shi bayan nayi nasara, wata kuma ta zo ta ce ta yi soyayya da shi tsawon shekara 15;
wata kuma ta yi shekara ashirin da wani abu tare da shi, da dai sauransu.
Domin na fahimci ina kan wani shiri ne a rayuwarsa shi, Shiyasa nayi amfani da wasu dubarun da suka haɗa da samun damar ganin kiraye-kirayen wayarsa da saƙonni.