Ƴan Najeriya na ganin Hauka a APC — Inji Fitaccen Ɗan Jarida Bayo
Wani Fitaccen Ɗan Jarida Bayo Onanuga ya bayyana cewar ƴan Najeriya na ganin Hauka a Jam’iyyar APC.
Yayi jawabi akan rikicin daya faru akan Tikitin Tsayawa Takara da aka siyawa Tsohon Shugaban Ƙasa Goodluck Jonathan.
KARANTA WANNAN LABARIN: Haƙurin Ɗaliban Najeriya Ya Ƙare, Baza su Iya Haƙurin Makonni 12 A Gida ba — Gani Adams ga FG
Tsohon Shugaban Kamfanin Dillancin Labaru na Ƙasa yace ana siyasa ne amma babu tsari ko kaɗan a APC.
Onanuga yayi Allah wadai da yadda ake ƙarfafar gwuiwar kowane sakarai ya nemi Takarar Shugaban Ƙasa ciki har da “Dattijon da Jam’iyyar ta kora daga mulki a Shekarar 2015”.
Yace a ƙirgar da akayi yanzu mutane 26 nason su gaji Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, duk da akwai yiwuwar ƙarin wasu masu sayen Tikitin.
Mai Mallakin Mujallar News Yayi nuni dacewar “ana buga wasa” wanda hakan ya tuna mashi tsohon shugaban Najeriya Ibrahim Babangida.