Ƴan Sanda sun cika hannu da ɓarayin Raguna 132 a Naija
An kama wasu mutane uku da laifin satar raguna 132 a karamar hukumar Mashegu da ke jihar Neja.
Wadanda ake zargin dai sun hada da Mohammed Abdullahi Chumo mai shekaru 30 dan Ukoro jihar Kwara da Aliyu Salihu mai shekaru 20 dan garin Gwadabawa na jihar Sokoto da kuma Arzika Ahmadu mai shekaru 25 shima dan asalin garin Gwadabawa na jihar Sokoto.
KARANTA WANNAN LABARIN:Yadda rikicin El-Rufa’i da Uba Sani ya fara raba wasu da kujerun su a Kaduna
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Neja, SP Wasiu Abiodun, ya ce wadanda ake zargin sun amsa laifin ne a lokacin da ake yi musu tambayoyi.
Ya bayyana cewa sun hada baki tare da yin awon gaba da raguna 132 daga cikin mutane biyu da aka kashe da ke kiwo a kusa da unguwar Manigi da ke karamar hukumar Mashegu.
“Abin farin ciki, a ranar 14 ga Maris, 2024, daya daga cikin wadanda abin ya shafa ya hangi wani dan kungiyar, Chumo, a Kasuwar Zungeru dauke da ragunan guda shida a kokarin sayar da su. Wanda abin ya shafa ya daga murya,” in ji Abiodun.
Ya bayyana cewa, nan take aka kama wanda ake zargin sannan ya jagoranci tawagar ‘yan sanda zuwa kauyen Jimi inda ake ajiye sauran raguna.
Daga baya an kama Aliyu da Arzika.
An mika wadanda ake zargin zuwa sashin Crack Squad na rundunar ‘yan sanda domin gudanar da bincike mai zurfi da kuma tuhume su.
Kakakin ‘yan sandan ya kara da cewa, an saki ragunan ga mai hakki.
A wani labarin kuma:Nan bada jimawa ba Sojoji zasu ida fatattakar ƴan ta’adda a Najeriya – Lagbaja
Babban hafsan sojin Najeriya Laftanar Janar Taoreed Lagbaja, ya jaddada kudirin rundunar sojin Najeriya, da jajircewarsu wajen ganin an fatattaki ‘yan tada kayar baya, da ‘yan fashi da makami, da duk wani nau’in wuce gona da iri da ke kawo cikas ga zaman lafiyar kasar.
Lagbaja ya bayar da wannan tabbacin ne a sakonsa na Easter ga dakarun sojin Najeriya ranar Lahadi a Abuja.