Ƴan sanda sun dakile yunkurin garkuwa da mutane sau 2, sun kuɓutar da mutane 5 a Katsina
Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta dakile yunkurin yin garkuwa da mutane guda biyu a kananan hukumomin Kankara da Faskari, inda ta ceto jimillar mutane biyar daga hannun ‘yan bindiga.
Kakakin rundunar ‘yan sandan, ASP Abubakar Sadiq Aliyu ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar, inda ya ce lamarin na farko ya faru ne a ranar 14 ga watan Janairu da misalin karfe 1:45 na dare lokacin da wasu ‘yan bindiga suka kai farmaki kauyen Baguma da ke karamar hukumar Kankara suka yi awon gaba da wasu mazauna kauyen guda biyu – Garba Musa 50, da Bala Disco, 54.
KARANTA WANNAN LABARIN:Da Ɗuminsa: An ceto ƴan uwan marigayiya Nabeeha
Da take amsa kiran gaggawar, tawagar karkashin jagorancin jami’in ‘yan sanda DPO Hassan A. Musa na Kankara sun yi ta harbin bindiga, inda daga bisani suka kubutar da mutanen biyu da aka yi garkuwa da su.
Bayan kwana hudu, a ranar 18 ga watan Janairu da misalin karfe 12:30 na rana, wani direba mai suna Abdullahi Idris, mai shekaru 50, daga karamar hukumar Dala, ta jihar Kano, yana jigilar fasinjoji uku – Jamilu Dahiru (30), Machido Abubakar (25), da Aisha Muhammad (55). – daga jihar Zamfara zuwa Kano lokacin da wasu ‘yan bindiga suka yi musu kwanton bauna a hanyar Sheme zuwa Kankara.
A cewar ASP Sadiq, ‘yan bindigar sun yi yunkurin yin garkuwa da dukkan mutane hudu da ke cikin motar amma sai suka gamu da gaggawa daga tawagar da DPO na hedikwatar sashin Faskari ya jagoranta.
A irin wannan bajintar jami’an sun yi artabu da ‘yan bindigar, inda suka samu nasarar kubutar da duk wadanda aka yi garkuwa da su.
Da yake yabawa kwazon jami’an sa, kwamishinan ‘yan sandan jihar Katsina, CP Aliyu Abubakar Musa, ya bukaci jama’a da su ci gaba da baiwa ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro bayanai kan lokaci, domin saukaka daukar matakin gaggawa kan ayyukan miyagun laifuka a jihar.
Ya nanata kudurin rundunar na tabbatar da tsaro ga daukacin mazauna Katsina.
A wani labarin kuma:Wata Sabuwa: An ƙaryata labarin korar Daraktocin hukumar tattara haraji ta Kano
Hukumar gudanarwar hukumar kula da tattara kuɗaɗen haraji ta jihar Kano ba ta karyata korar wasu Daraktocinta guda takwas, inda ta bayyana labarin a matsayin na bogi da tsantsar karya da aka kirkira domin kawo rudani.
Kafafen yada labarai na yanar gizo sun ruwaito cewa hukumar tara kudaden shiga ta kori daraktocinta bisa almubazzaranci da kudade amma hukumar a cikin wata sanarwa da mataimakin daraktan ma’aikatan gwamnati Rabiu RiminGado ya sanyawa hannu ta ce labarin ba shi da tushe balle makama.