Ƴan sanda sun Damƙe Ƴan Ƙungiyar Asiri A Legas
Rundunar Ƴan Sandan Jahar Legas ta kama wasu mutane huɗu da ake zargin ƴan ƙungiyar asiri ne.
Ana tuhumar su da aikata munanan laifuka da aikata laifuka a yankin Badagry da ke jihar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Abiodun Ya Kori Ɗan Kwangila, Ya Ba FG Makonni Biyu Ta Gyara Titin Legas-Abeokuta.
Jami’in hulda da jama’a na Rundunar Ƴan Sandan Jahar, SP Benjamin Hundeyin ya tabbatar da kamen su a wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar.
Kakakin ya ce Rundunar ta samu ƙorafe-ƙorafe da dama daga mazauna yankin game da tashin hankali da kashe-kashe.
“An kama su ne a sassa daban-daban na Badagry a wani samame da suka kai kwanaki.
“Bincike na farko ya nuna cewa waɗanda ake zargin ƴan ƙungiyar Asiri ne ta Eiye da Aiye confraternities ne”, in ji Hundeyin.
Za a gurfanar da wadanda ake zargin zuwa kotu bayan kammala bincike.
Kwamishinan ƴan sanda, Abiodun Alabi ya tabbatar da cewa hukumar tsaro za ta ci gaba da yakar ƙungiyoyin asiri da masu aikata laifuka