Ƴan sanda sun damƙe wasu Ma’aurata da sace ɗan maƙwabcin su
Rundunar ‘yan sandan jihar Nasarawa ta cafke wani mutum da matarsa bisa zargin satar dan makwabcin su dan shekara biyu.
DSP Ramhan Nansel, jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan ne ya bayyana hakan a jiya, a garin Lafia yayin da yake zantawa da manema labarai.
KARANTA WANNAN LABARIN:An Samu Asarar Rayuka Yayinda Jirgin Ruwa Ya Kife A Jahar Nasarawa
Nansel ya ce mahaifin wanda abin ya shafa, Adamu Abdullahi na kasuwar Orange, Mararaba, karamar hukumar Karu, ya kai rahoto ga ‘yan sanda a ranar 13 ga watan Agusta da misalin karfe 3:30 na rana cewa dan nasa mai shekaru biyu da haihuwa ya bace kusan makonni biyu. .
Ya ce wanda ya shigar da karar ya kuma shaida wa ‘yan sanda cewa a ranar ne wani da ba a san ko wane ne ba ya kira shi ta wayar tarho inda ya bukaci a biya shi kudin fansa naira miliyan biyu.
Kakakin ya ce, nan take aka tura jami’an ‘yan sanda domin neman yaron da ya bata, kuma kokarin da suka yi ya kai ga cafke babban wanda ake zargi da kuma wasu mutane uku.
A cewarsa, babban wanda ake zargin, wanda makwabci ne ga mahaifin wanda aka sace, bayan da aka yi masa tambayoyi, ya amsa cewa ya hada baki da sauran wadanda ake zargin, dukkansu na kasuwar Orange, don sace yaron.
Ya kara da cewa wanda ake zargin ya kuma bayyana wa jami’an ‘yan sanda cewa ya mika yaron ga matarsa, inda ta kai shi jihar Katsina.
Nansel ya ce ‘yan sanda sun bi sawun matar zuwa jihar Katsina, inda suka kama ta tare da kwato yaron, inda suka hada su da iyayensa.
Kakakin ya kuma ce rundunar ta kama mutane 14 a tsakanin watan Yuli zuwa Agusta bisa laifuka daban-daban da suka hada da garkuwa da mutane, fashi da makami da kuma kungiyoyin asiri.
A wani labarin kuma:Ni Nake Hana Sojojin ECOWAS Afkawa Kasar Nijar–Tinubu
Shugaba Bola Tinubu ya bukaci ‘yan Najeriya da su kada kuri’ar kin amincewa da gwamnonin da ke gudanar da ayyukan da ba su gamsu dasu ba.
Da yake jawabi a fadar shugaban kasa a ranar Alhamis, shugaban ya bukaci ‘yan Najeriya da su yi wa gwamnoninsu hisabi a ranar zaɓe.