Ƴan Sanda sun hallaka Ƴan Ta’adda 2, tare da Ƙwato makamai a Kaduna
Jami’an Rundunar Ƴan Sandan Jahar Kaduna sun hallaka ƴan ta’adda guda biyu a ƙauyen Kimbi ta Ƙaramar Hukumar Birnin Gwari dake Jahar
“A ƙoƙarin na yaki da ƴan bindiga akan ƴan ta’adda a Kaduna musamman a Birnin Gwari, Rundunar a ranar 31 ga watan Mayu na Shekarar 2022, ta samu nasarar hallaka ƴan bindiga biyu, tare da samo bindigun su, a yayinda wasu suka samu raunuka.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ecuador vs Nigeria: Super Eagles ta rasa wasan ta a hannun Peseiro karo na biyu
“Wannan ya biyo bayan kiran gaggawa da aka samu a ranar da misalin ƙarfe 4 na rana cewa wasu ƴan bindiga sun kai hari a ƙauyen Kimbi ta Ƙaramar Hukumar Birnin Gwari domin yin garkuwa da mutane.
“Rundunar tayi saurin tura Jami’an zuwa wurin domin kai masu hari, inda suka yi musayar wuta, inda aka samu nasarar kashe ƴan bindiga 2 da ƙwato bindigogi ƙirar Ak-47 guda biyu a wurin su.
Comments 1