Ƴan Sanda sun hallaka riƙaƙƙun masu garkuwa da mutane a Delta
Rundunar Ƴan Sandan Jahar Delta ta samu nasarar bindige masu garkuwa da mutane guda uku a Jahar.
Mai Magana da Yawun Rundunar Ƴan Sandan Jahar Bright Edafe ya Tabbatar da haka a cikin wata sanarwa daya fitar a ranar Litinin a Asaba, Babban Birnin Jahar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Da-Dumi-Dumi: Wani dan bindiga ya harbe ministan Jamhuriyar Dominican har lahira
Yace “a ranar 5 ga watan yunin Shekarar 2022 da misalin ƙarfe 12:35 Jami’an kai ɗaukin Gaggawa na Rundunar a lokacin da suke aikin samame akan masu garkuwa da mutane akan hanyar Asaba/Benin, wasu ƴan bindiga da ake kyautata zaton Masu garkuwa da mutane da yawan su yakai 5, sun fito daga wani dajin Umunede.
“Ƴan bindigar sun buɗe wuta a ƙoƙarin su na yin sata tare da garkuwa da mutanen, amma rashin sanin su shine mazauna cikin motar, Ƴan Sanda ne.
“Tawagar tayi wani yunƙurin gaggawa tare buɗe masu wuta. A lokacin ƴan bindigar suka gano cewa ƴan sanda a cikin Motar sai suka ruga zuwa Daji.
“Ƴan Sandan sun bi bayan su a musayar wutar tare da yi masu mummunan rauni, inda akayi gaggawar kaisu Asibiti, amma sun rasu suna karɓar magani.”
Edafe yace sun ƙwato Fistin ɗaya, da Harsashi mai nauyin 7.62mm guda 6, da wani da aka riga aka sanya a bindigar guda 4.
Comments 1