Ƴan sanda sun kama ɓarawon mota a Nasarawa
Rundunar ‘yan sandan jihar Nasarawa ta yi nasarar cafke wani da ake zargin barawo ne mai suna Yusuf Isah, tare da kwato wata mota da aka sace a karamar hukumar Nasarawa.
An tabbatar da kamun ne a wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar, DSP Ramhan Nansel, ya fitar ranar Lahadi.
KARANTA WANNAN LABARIN:Sojojin Najeriya na iya murkushe ƴan ta’adda – Gwamna Sule
“A ranar 23 ga Fabrairu, 2o24, da misalin karfe 11:24 na safe, wata mata Aisha Usman ta kwalejin kimiyya dake, Nasarawa ta shigar da kara a sashin Nasarawa inda ta ce ta ajiye motarta, wata jar Toyota Corolla mai lamba NSW 949 PJ, a ofishin harabar makarantar Sakandare ta Gwamnati, ta babbar kasuwar Nasarawa kuma daga baya aka gano an dauke ta.
“Bayan samun korafin, an fara farautar wanda ake zargin tare da kwato motar da aka sace.
Saboda haka, an kira ‘yan sanda, kuma aka kama wanda ake zargin, kuma an kwato motar daga gare shi a matsayin abin bayyani,” in ji sanarwar.
Nansel ya bayyana cewa kwamishinan ‘yan sanda Umar Shehu Nadada, yayin da yake yaba wa kokarin jama’a na goyon bayansu, ya tabbatar musu da irin jajircewar da rundunar take yi na kare lafiyar su.
A wani labarin kuma:An tsaurara matakan tsaro yayin da ake ci gaba da shari’ar Nnamdi Kanu
Akwai manyan jami’an tsaro a babbar kotun tarayya da ke Abuja, inda gwamnatin tarayya za ta ci gaba da shari’ar da ake yi wa shugaban masu fafutukar kafa kasar Biafra, IPOB, Nnamdi Kanu.
Jami’an tsaro dauke da makamai sun killace dukkanin hanyoyin da suke isa kotun da ke gefen hedikwatar ma’aikatar shari’a ta tarayya.