Ƴan sanda sun kama ɗan ƙungiyar asiri ɗauke bindiga a Edo
Jami’an rundunar ‘yan sandan jihar Edo sun kama wani da ake zargin dan kungiyar asiri ne mai suna Endurance Ezeigbe Otansowe da bindiga.
Majiyar Jaridar Dimokuraɗiyya ta ba rahoto cewa kakakin rundunar, Chidi Nwabuzor, wanda ya bayyana hakan ga manema labarai a Benin, ya ce rundunar ‘yan sandan Evbotubu ta kama wanda ake zargin ne a ranar 12 ga Afrilu, 2024 bayan rahoton sirri.
KARANTA WANNAN LABARIN:Yanzu-Yanzu: An yanke wa Bobrisky hukuncin daurin kurkuku
A cewarsa, jami’in ‘yan sanda reshen da ke kula da Evbotubu ya samu bayanai game da ayyukan kungiyar asiri, wanda ya sa aka tsaya ana bincike a yankin.
“A yayin aikin, ‘yan sanda sun kama wanda ake zargin da bindigar Branil daya,” in ji shi.
A cewarsa, wanda ake zargin a yayin bincike ya tabbatar da cewa yana da haramtaccen makami.
Ya ce za a gurfanar da wanda ake zargin a kotu.
A wani labarin kuma:Amurka ta yi taron G7 kan harin da Iran ta kai wa Isra’ila
Shugaban Amurka Joe Biden ya ce za a yi taron kasashen G7 a ranar Lahadi (yau) don daidaita martanin diflomasiyya guda daya kan harin da Iran ta kai wa Isra’ila.
DAILY POST ta tuna cewa Iran ta kai wa Isra’ila hari a matsayin ramuwar gayya kan harin da ya kashe wani kwamandan sojojin Iran a Damascus a farkon watan Afrilu.