Ƴan sanda sun tsare jami’in da ya harbe direban mota
Rundunar ‘yan sandan jihar Delta ta ce an kama wani jami’in da har yanzu ba a tantance ba, wanda ake zargi da harbin wani direban mota a wani faifan bidiyo daya bazu.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Delta, DSP Bright Edafe, wanda ya bayyana hakan a wani sako da ya wallafa a shafin sa na X, ya bayyana rashin jin dadinsa kan rashin da’a da jami’in ya yi.
KARANTA WANNAN LABARIN:PDP ta Bada Umarnin Janye Duk Wasu Kararrakin Jam’iyyar da Ke Gaban Kotuna
DAILY POST ta samu cewa jami’in da ya yi kuskuren da ya tsaya yana bincike a kan titin Gabas zuwa Yamma, cikin garin Ughelli, ya bude wuta kan wanda abin ya shafa bayan gardama.
Direban motar da har yanzu ba a san ko wane ne ba, kamar yadda faifan bidiyon ya nuna, an harbe shi a kafa da ciki.
Da yake tura bidiyon a shafinsa na X, PPRO ya ce, “Rundunar ‘yan sandan Najeriya ba ta kuma amince da rashin da’a daga kowane ma’aikaci ba.
“A kan wannan batu, kwamishinan ‘yan sanda, CP Wale Abass ya ba da umarnin a tsare babban sufeton ‘yan sandan da ya yi kuskure.
“Wadanda aka jikkata na samun kulawa. A halin da ake ciki, CP ya bukaci jama’a da su kwantar da hankalinsu, domin ya ba da tabbacin yin adalci,” inji shi