Ƴan Sandan Jahohi zai magance matsalolin tsaro — Afenifere ta gayawa Buhari, Gwamnoni
Ƙungiyar Ƴan Asalin Yarbawa ta Pan Yoruba, Afenifere ta koka kan yawaitar matsalolin tsaro da ka iya haddasa samun ƴan gudun hijira a yankin Kudu.
Ƙungiyar tayi kira ga Gwamnatocin Tarayya da Jahohi da Hukumomin tsaro dasu kawo ƙarshen matsalar tsaro da ake fuskanta a Ƙasar, domin magance samun irin sansanin gudun hijira a Arewa zuwa yankin na Najeriya.
KARANTA WANNAN LABARIN: Shugaban Karamar Hukuma A Kano Ya Raba Tallafin Kayayyaki Na Naira Miliyan 50
Ƙungiyar ta bayyana haka a cikin wata sanarwa da Mai Kula da Yaɗa Labarun ta Jare Ajayi ya sanyawa hannu, ta ayyana kiran da Gwamnatin Jahar Zamfara tayi na ƴan Ƙasa su kare kawunan sa ta hanyar ɗaukar makamai a matsayin gazawar ta kai tsaye daga ɓangaren Gwamnati.
Afenifere tayi kira ga Gwamnonin jihohi dasu haɗu da Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari da Shuwagabancin Majalisun Najeriya akan buƙatar su kafa ƴan Sandan Jihohi a matsayin abinda ya zama dole.
Ƙungiyar ta ƙara dacewa idan dukkanin Jahohi 36 ba zasu amince a ƙirƙiri Ƴan Sandan Jihohi, to na Kudu suje Abuja, tare da tabbatar da cewa anyi Ƴan Sanda.