Ƴan Takara 3 kaɗai suka cancanta su nemi Kujerar Shugaban Ƙasa — Cewar wani Lauya
Kayode Ajulo wani Fitaccen Lauya ya bayyana damuwar sa na yawaitar ƴan Takarar Kujerar Shugaban Ƙasa a Babban Zaɓe na Shekarar 2023.
A cewar Ajulo, ƴan Takara 3 a Jam’iyyar APC Suka cancanta su nemi Kujerar Shugaban Ƙasa.
KARANTA WANNAN LABARIN: Matan Afghanistan Sun Yi Zanga-zangar Rashin Amincewa Da Dokar Rufe Fuska
Ya bayyana haka a tattaunawar sa da Kamfanin Dillancin Labaru na Ƙasa a ranar Talata a Abuja.
“Daga binciken da muka gudanar na ƴan Takara, ƴan Takara uku kaɗai a Jam’iyyar APC Suka cancanta su nemi Kujerar Shugaban Ƙasa,” cewar Ajulo.
Daga cikin ƴan Takarar akwai Mataimakin Shugaban Ƙasa Yemi Osinbajo, da Tsohon Gwamnan Jahar Lagos Bola Tinubu.
Ajulo ya bayyana cewar baya mamaki na yadda ƴan Takara ke son Yiwa Najeriya aiki, yana mai cewa yawan yayi nisa sosai.
Ajulo yace bayan an tantance ƴan Takara za’a tabbatar da waɗanda suka cancanta su jagoranci Zaben Fidda Gwani domin tunkarar Zaɓe.