Ɗa Ɗuminsa: EFCC na neman tsohon gwamnan Kogi, Yahaya Bello ruwan a jallo
Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati, EFCC, ta bayyana tsohon gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello a matsayin wanda take nema ruwa a jallo.
Hakan ya biyo bayan gazawar tsohon gwamnan ne ya gurfana gaban mai shari’a Emeka Nwite na babbar kotun tarayya Abuja a ranar Alhamis domin gurfanar da shi a kan zargin karkatar da kudi har N84bn.
KARANTA WANNAN LABARIN:Yahaya Bello ya roki kotu da ta hana kama shi
A wani sako da ta wallafa a shafinta na Facebook a ranar Alhamis, hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta bukaci ‘yan Najeriya dasu bada bayanai game da inda Bello yake tare da kai rahoto ga ofishin ‘yan sanda mafi kusa.
Sanarwar ta ce, “EFCC ta bayyana tsohon gwamnan Kogi Yahaya Bello a matsayin wanda take nema ruwa a jallo, Hukumar EFCC na neman tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, bisa laifukan da suka shafi tattalin arziki da kudi har naira biliyan 80.2.
“Duk wanda ke da labarin inda yake to ya kai rahoto ga Hukumar ko kuma ofishin ‘yan sanda mafi kusa.”
A ranar Larabar da ta gabata ne jami’an hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC, Department of State Service), ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro suka yi wa gidan Bello na Abuja kawanya.
Sai dai gwamnan jihar Kogi mai ci Usman Ododo ne ya zare shi daga ginin.
A wani labarin kuma:Clark ya bukaci PDP da ta binciki Wike kan yiwa jam’iyyar zagon ƙasa
Tsohon kwamishinan yada labarai na tarayya kuma shugaban ƙungiyar kudu maso kudu, Cif Edwin Clark, ya bukaci kwamitin ladabtarwa da zai binciki zargin cin hanci da rashawa da ake zargin tsohon gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, da wasu da rawar da jam’iyyar ta PDP ta yi a baya PDP, a zaben 2023.
A wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba a Abuja, Clark ya ce Wike, wanda shi ne Ministan Babban Birnin Tarayya, FCT, shi ne babban makiyin PDP, inda ya yi amfani da ita da nufin ruguza ta.