Ɗalibai 15,000: NANS na neman Gwamnatin Tarayya da ta sassauta haramcin digirin ƙasashen waje
Kungiyar dalibai ta kasa NANS a jamhuriyar Benin ta bayyana cewa sama da dalibai 15,000 a kasar ne suka shiga halin kaka-ni-kayi da dokar hana karatu a ƙasashen.
A dalilin haka ne NAN ta yi kira da a sassauta dokar hana tabbatar da shaidar digiri daga kasar da Togo.
KARANTA WANNAN LABARIN:Gwamnatin Tarayya ta sanar da hanyoyin da za ta sayar da gidaje
Kwanan nan ne wani dan jarida mai bincike ya fallasa yadda ake yin satar takardar shedar a makarantu a kasashe makwabta.
A ci gaban da aka samu, gwamnatin Najeriya ta sanar da hana tabbatar da shaidar digiri daga kasashen.
Sai dai da yake bayyana a gidan Talabijin na Channels a ranar Alhamis, Shugaban NANS na Jamhuriyar Benin, Ugochukwu Favor, ya ce kamata ya yi gwamnati ta duba daliban da idon rahama.
“A yanzu, zan ce ya kamata Gwamnatin Tarayya ta duba lamarin. Yanzu, ba za ku iya ba, saboda abin da ke faruwa a wannan makarantar, ku hukunta kowa saboda ya shafi kusan ɗalibai 15,000 a Jamhuriyar Benin.
“Ni ban tabbatar ba idan hakan ya dade yana faruwa. Wannan shi ne irin abin da ya fito a shafukan sada zumunta kuma muna kokarin gano tsawon lokacin da abin ya faru,” in ji shugaban NANS.
“Don haka, shi ya sa na kafa kwamiti a matsayina na shugaban kasa domin ya binciki shi.
A wani labarin kuma:Rundunar ƴan sandan Najeriya ta fara tantance masu neman aiki
Rundunar ‘yan sandan Najeriya reshen jihar Nasarawa, ta fara aikin tantance masu neman aiki a hukumance.
Wannan sanarwar ta fito ne ta wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan, DSP Ramhan Nansel, ya fitar a madadin kwamishinan ‘yan sanda, CP Umar Shehu Nadada.