Omoyele Sowore, ɗan takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam’iyar AAC, ya ce shi ne shugaban ƙasa mai jiran gado idan Muhammadu Buhari ya sauka.
Ya kuma roki ƴan ƙasa a kan su yi farin ɗango a zaɓen shugaban ƙasa su zaɓi jam’iyar sa ta AAC.
KARANTA WANNAN LABARIN: Sabon Hari: An Kashe Mutum tare da Garkuwa da wasu 20 a Filato
Sowore, wanda shi ne mamallakin jaridar nan ta SaharaReporters, ya yi wannan kira ne a Akure a jiya Asabar a yayin da ya ke ganawa da manema labarai, inda ɗumbin magoya baya su ka tarbe shi.
A cewar sa, ƴan Nijeriya, musamman matasa, dole su tashi tsaye domin su kwaci ƴancin su a zaɓe mai zuwa
Ya ce 2023 shekara da za ta baiwa matasa damar tumɓuke masu mulki su hau kujerar sabo da su ne masu jini a jika da kuma tunani da hikimomi na zamani ba na da ba.
“Lokacin da za a gyara Nigeria ya zo wa ƴan Nijeriya,” in ji shi.