Tsohon Shugaban Kasa, Janar Abdulsalami Abubakar (Mai Ritaya), ya bukaci matasa da su nuna sha’awarsu da tsayawa takarar mukamai a Babban zabe kasa Mai zuwa na shekarar 2023.
Ya yi wannan kiran ne a ranar Juma’a a lokacin da ya karbi bakuncin dan takarar shugaban kasa a 2023, Prince Adewole Adebayo, a gidansa da ke Minna, babban birnin jihar Neja.
Adebayo wanda shi ne shugaban gidan talabijin na Kaftan, ya samu rakiyar tsohon ministan wasanni Solomon Dalung da dai sauransu.
“Hakika Najeriya na bukatar Matasa da za su karbe ragamar mulki daga hannunmu na manya. Ina matukar farin ciki da cewa ba ku kadai ba, sauran matasa suna nuna sha’awar karbar ragamar shugabancin kasar nan,” in ji Abdulsalami.
A nashi bangaren Adebayo da yake jawabi ya yabawa Abdulsalami bisa kokarin da ya yi na ganin al’ummar kasar sun dawo tafarkin dimokuradiyya a watan Mayun 1999.
“Dalilin da ya sa na fito yana da mahimmanci domin kasar kanta tana bukatar ceto a yanzu kuma mutane irin ku sun yi kasada da rayuwar ku a zahiri kuma kun yi asarar ‘yan uwanku da dama. Ko da kasar ba ta kai ga cimma burinta ba,” inji shi.