2023 AFCON: Zamu sanya farin ciki ga ƴan Najeriya – Musa ya yi magana kan wasan Super Eagles da Guinea-Bissau
Kyaftin din Super Eagles, Ahmed Musa ya ce kungiyar za ta yi kokarin faranta wa ‘yan Najeriya rai ta hanyar samun nasara a kan Guinea-Bissau ranar Juma’a.
‘Yan Afirka ta Yamma za su yi kokarin kara inganta damar samun gurbi a gasar cin kofin Afrika ta 2023 lokacin da za su kara da Djurtus a karawarsu ta uku a filin wasa na Moshood Abiola, Abuja.
KARANTA WANNAN LABARIN:Jirgin Saman Najeriya Zai Fara Tashi Kafin Ranar 29 Ga Watan Mayu – FG
A daidai wannan lokaci ne a shekarar 2022, Super Eagles ta yi kunnen doki 1-1 da Black Stars ta Ghana ta yi rashin samun gurbin shiga gasar cin kofin duniya ta FIFA 2022 a Qatar.
Musa wanda a halin yanzu yana taka leda a kulob din Sivasspor na kasar Turkiyya.
“Mun san abin da ya faru shekara guda da ta wuce a nan da Ghana. Wannan yana binmu yanzu. Wannan ita ce wasan share fage na AFCON kuma muna son farantawa magoya bayanta rai,” in ji Musa a wani taron manema labarai da DAILY POST ta sanyawa ido.
“Mun san wahalhalun da ake fama da su a kasar nan da kuma harkar kwallon kafa ita ce kadai abin da ke hada kan ‘yan Najeriya. Muna son mu faranta musu rai”.
Super Eagles ce ke kan gaba a rukunin B da maki shida a wasanni biyu, yayin da Guinea-Bissau ke matsayi na biyu da maki hudu daga wasanni iri daya.
A wani labarin kuma:Sarakunan Kano, Gaya sun taya zababben Gwamnan jihar murna
Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero da na Masarautar Gaya Aliyu Ibrahim Gaya sun taya zababben gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf murnar nasarar da ya samu a zaben da ya gudana a ranar Asabar.
A wata wasika da ya aike wa zababben gwamnan, Bayero ya bayyana cewa al’ummar kasar sun amince da tsarin mulkin dimokradiyya.