Uwargidan shugaban kasa, Aisha Buhari, ta bukaci daukacin ‘ya’yan jam’iyyar APC mai mulki da su kara kaimi wajen tabbatar da nasarar Tinubu da Shettima na takarar shugaban kasa a zaben 2023 mai zuwa.
Misis Aisha Buhari na magana ne a ranar Alhamis lokacin da ta kaddamar da kungiyar Mata da Matasan APC na kungiyar yakin neman zaben Tinubu da Shettima a Ilorin, jihar Kwara.
KARANTA KUMA Tinubu Ya Nada Aisha Buhari A Matsayin Shugabar Kwamitin Kamfen Ta mata
Jaridar DIMOKURADIYYA ta rawaito cewa Ta bayyana cewa jam’iyyar ta gudanar da yakin neman zabe na musamman a lokacin yakin neman zabe na 2015 da 2019 kuma ta kuduri aniyar yin hakan tare da tabbatar da samun nasara a zabe mai zuwa.
“Kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na mata da matasa ya zama wani yunkuri ta hanyar nuna cewa su ne masu kawo canji, inda suka jagoranci yakin neman zabe wanda ya kai ga samun nasara ga APC a zaben shugaban kasa na 2015.
“Nasarar ta samo asali ne daga jajircewar matasa maza da mata na jam’iyyarmu da suka fito da yawan kuri’u da ba a taba ganin irinsu ba domin zaben jam’iyyarmu a zabukan shugaban kasa na 2015 da 2019 kuma muna fatan tarihi zai maimaita kansa a zaben 2023.
Ta kuma bukaci mata da matasan jam’iyyar APC da su ci gaba da dorewar kwarin gwiwa da aka yi amfani da su a yakin neman zabe da suka gabata ta hanyar tabbatar da yakin neman zabe na gida-gida domin samun nasarar jam’iyyar a zaben.
A yayin da take mika tutar jam’iyyar ga Misis Oluremi Tinubu domin fara yakin neman zabe a fadin kasar, uwargidan shugaban kasar ta bukace ta da ta hada kai da dukkan mambobinta tare da gudanar da yakin neman zabe don ganin an samu nasara. (NAN)
A Wani Labarin Kuma Sokoto Ta Samu Lambar Yabo Da Girmamawa Ta Uku Daga Bankin Duniya
Gwamnatin jihar Sokoto ta samu lambar yabo ta girmamawa guda uku daga bankin duniya na ci gaba da aiwatar da himma wajen aiwatar da ayyukan da bankin duniya ke taimaka wa Jihohi na nuna gaskiya da rikon amana da dorewar shirin (SFTAS).
Mukaddashin kwamishinan kudi na jihar Dr Mohammed Inname ne ya bayyana hakan ga manema labarai ranar Alhamis a Abuja.