….Dan takarar gwamna a jam’iyyar APC na Kano Nasiru Gawuna ya yabawa da yadda ake zabe cikin
Alhaji Nasiru Gawuna mataimakin gwamnan jihar Kano kuma dan takarar gwamna a jam’iyyar APC ya yaba da yadda zaben ya gudana cikin kwanciyar hankali da lumana.
Gawuna, wanda ya kada kuri’a a Makarantar Kur’ani da ke unguwar Gawuna da misalin karfe 9:50 na safiyar ranar Asabar, ya yaba wa masu ruwa da tsaki kan yadda aka gudanar da zaben cikin zaman lafiya ya zuwa yanzu.
Jaridar DIMOKURADIYYA ta tattaro cewa Dan takarar ya kuma yi addu’ar samun zaman lafiya da kwanciyar hankali kafin zabe da lokacin zabe da kuma bayan zaben.
KARANTA HAKANAN Wasu Limaman Juma’a Sun Yi Khudubar Muhimmancin Zaben Gawuna
Dan takarar gwamnan ya kuma nuna jin dadinsa kan yadda masu kada kuri’a suka fito a rumfar zaben.
“Fitowar jama’a na da ban sha’awa saboda kuna ganin cewa mutane da yawa sun riga sun zo don kada kuri’unsu,” in ji shi.
Ya bayyana kwarin gwiwar cewa zai yi nasara a zaben.
Ya kuma yabawa INEC da ta gyara wasu batutuwan da aka taso da kuma cikas a lokacin zaben shugaban kasa.
Gawuna ya samu rakiyar matarsa Hajiya Hafsat Gawuna.
Kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa, akwai gagarumin tsaro a wuraren rabon kayayyakin da hadin gwiwar tawagar ‘yan sanda da jami’an NSCDC suka samar.
Jaridar DIMOKURADIYYA ta kuma ruwaito cewa an fara kada kuri’a a rumfunan zabe da dama a wasu sassan birnin da misalin karfe 8:30 na safe tare da fitowar mata da dama. (NAN)
A Wani Labarin Kuma Jami’an ‘Yan Sanda Sun Ceto Ma’aikatan INEC 19 Da Aka Yi Garkuwa Da Su
Jami’an ‘yan sanda a jihar Imo sun ceto wasu ma’aikatan hukumar INEC 19 da aka yi garkuwa da su da sanyin safiyar Asabar a jihar Imo.
Jaridar DIMOKURADIYYA ta tattaro cewa Hukumar INEC ta jihar ne suka tabbatar da faruwar lamarin.