Tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose, ya dage cewa dole ne yankin kudancin Najeriya ya samar da shugaban kasar a 2023.
Fayose, wanda ya taba zama gwamna har sau biyu a karkashin jam’iyyar PDP, ya bayyana hakan ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter a ranar Laraba, inda ya danganta hujjar sa kan kundin tsarin mulkin jam’iyyar.
“Tsarin mulkin PDP ya tanadi shugabancin karba-karba. Sashi na 3 (c) ya tanadi cewa jam’iyyar za ta ci gaba da manufofinta ta hanya “biyar da manufofin karba-karba na jam’iyya da kuma ofisoshin zaben jama’a don bin ka’idar daidaito, adalci da gaskiya,” in ji Fayose.
“Shugaban Najeriya na yanzu shine Shugabancin Arewa na wa’adi 2, don haka yana nuna cewa dole ne ya zama Shugabancin Kudu a 2023 ko ba komai. ‘Yan Najeriya su jira cikakken bayani nan ba da jimawa ba.”
Fayose wanda ya tsaya takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP ya sha kayi a hannun tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abukar a zaben fitar da gwani da aka gudanar a farkon watan nan.
Ya na daya daga cikin masu fafutukar ganin an sauya mulki zuwa kudancin Najeriya duk da jam’iyyar ta tabbatar da Atiku daga yankin Arewa, a matsayin dan takarar jam’iyyar.
Gwamna Nyesom Wike na Jihar Ribas, wanda shi ma ya sha kaye a zaben fidda gwani, ya yi neman zabe, da dai sauransu, bisa la’akari da yadda za a sauya mulki zuwa kudu.
Dimokuradiyya ta rawaito cewa jam’iyyar APC mai mulki ta tsayar da dan kudu – Bola Tinubu – a matsayin dan takararta na shugaban kasa domin girmama yarjejeniyar raba madafun iko da ake kira shiyyar arewa da kudu.