Wasu rahotanni daga jami’yyar APC reshen jihar Kano a Arewacin Najeriya na bayyana cewa gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje ya ayyana wanda zai yiwa jam’iyyar takarar gwamna a zaɓen shekarar 2023.
Majiyar Jaridar Dimokuraɗiyya ta Jaridar Popular News tace, Gwamna Ganduje wanda a ranar juma’a ya dawo daga wani taron tattalin arziki da masu zuba jari da ya gudana a haɗaɗɗiyar Daular Larabawa wato Dubai, ya fitar da wanda zai yi takarar gwamna a jam’iyyar APC, kuma nan gaba kaɗan zai bayyana sunan wanda ya ke muradin gadonsa.
Gwamna Abdullahi Umar Ganduje da Sanata Bashir Garba Lado lokacin da ya ke dawowa daga ƙasar Dubai.
KARANTA WANNAN LABARIN: 2023: Ni zan fara yin Mataimakiyar Shugaban Ƙasa a Najeriya — Yahaya Bello
Wata majiya daga fadar gwamnatin Kano, wacce ta buƙaci a sakaye sunanta ta bayyana cewa tuni Ganduje ya sauya tunanin marawa Abdulkarim Abdussalam Zaura baya wajen samun takara a jam’iyyar APC bisa wasu dalilai masu nasaba da siyasar cikin gida.
“Magana ta gaskiya mai girma Gwamna ya canza shawara akan goyon bayan A.A Zaura wajen samun takarar gwamnan Kano a jam’iyyar APC”.
Haka kuma majiyar ta ƙara da cewa Wasu daga cikin masu ruwa da tsaki a jam’iyyar APC sun yi kamun ƙafa ga Gwamnan da ya goyi bayan Zaura ɗin wajen samun takarar ɗan majalisar dattawa mai wakilatar Kano ta tsakiya, amma hakan bai kai ga nasara ba domin gwamnan ya nuna ra’ayinsa ga tsohon shugaban hukumar kula da ƴan gudun hijira ta Najeriya, Sanata Bashir Garba Lado.
“Akwai wasu manyan mutane a jam’iyyar APC da su ka buƙaci gwamnan ya goyi bayan A.A Zaura ɗin wajen samun takarar Sanatan Kano ta tsakiya a jam’iyyar APC, amma gwamnan ya nuna Bashir Garba Lado a matsayin wanda zai marawa baya”.
A.A Zaura dai ya taɓa takarar gwamnan Kano a tutar jam’iyyar GNP a zaɓen shekarar 2015. Sai dai daga bisani ya dawo cikin jam’iyyar APC.
Hakazalika Zaura, wanda ake ganin shi ne ya ke ɗaukar nauyin jam’iyyar APC a Kano, yana daga cikin waɗanda su ke kan gaba wajen neman jam’iyyar ta tsayar da su takarar kujerar gwa
Comments 1