An garkame ofishin yakin neman zaben Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP a jihar Ribas, Daily Post ta rawaito.
Kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar PDP reshen jihar Ribas ya ce an dauki matakin ne bisa umarnin gwamnatin jihar Ribas.
KARANTA WANNAN LABARIN: Shugaba Buhari Ya Yi Ta’aziyya Ga Adesina Bisa Rasuwar Mahaifiyarsa
An rufe ofishin da ke GRA Fatakwal da sanyin safiyar Juma’a.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Gwamnan jihar Ribas Nyesom Wike a makonnin da suka gabata ya sanya hannu kan dokar zartarwa mai lamba 22 wadda ta haramta ambaton ofisoshin yakin neman zaben da jam’iyyun siyasa ke yi a unguwanni ba tare da amincewar gwamnati ba.
Sai dai tawagar yada labarai na kungiyoyin yakin neman zabe na jam’iyyar PDP PCC reshen jihar Ribas, ta ce ta nemi amincewar gwamnatin jihar amma ba ta samu amsa ba tsawon makonni.
Don haka kungiyar ta yi Allah-wadai da matakin “saboda ya keta hakkinmu na ‘yancin fadin albarkacin baki.”
Har ila yau, ta ce: “Wannan gagarumin yunkuri na Gwamnatin Jihar Ribas, wanda aka gani a cikin siyasa, yana mayar da hankalin dimokuradiyyarmu da kuma mayar da jiharmu mai mahimmanci a siyasance baya lokacin da aka hade da sauran jihohin kasar.”
A wani labarin kuma, Shugaba Buhari Ba Zai Halarci Bikin Rantsar Da Ni Ba Idan Na Yi Nasara A 2023 – Sowore
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar African Action Congress, AAC, Omoyele Sowore ya ce shugaban kasa Muhammadu Buhari ba zai halarci bikin rantsar da shi ba bayan ya lashe zaben shugaban kasa na 2023.
Sowore ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a yayin da yake magana a wata hira da gidan talabijin na Vanguard a ranar Juma’a.