Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa ya gargadi dukkanin jam’iyyun siyasar jihar da su yi siyasa ta hanyar da za ta kara wa masu zabe kima, yana mai shan alwashin cewa gwamnatinsa ba za ta amince da siyasar ‘yan daba da adawa da rarrabuwar kawuna a fadin jihar ba.
Sule ya kuma yi kira ga jam’iyyun siyasa da su bi ka’idojin dimokuradiyya da bin doka da oda da kuma bin dokar zabe.
Da yake jawabi a wajen bikin murnar samun ‘yancin kai da kuma bikin cikar Najeriya shekaru 26 da samun jihar Nasarawa a ranar Asabar din nan, gwamnan ya bukaci ‘yan siyasa da su yi siyasa ba tare da bacin rai ba, ya kara da cewa, “Saboda a karshen duka za mu samu jihar Nasarawa guda daya wanda muke kira tamu”.
KARANTA KUMA: Gwamnan Narasawa: Ban San Kwamishinonina Ba Su Da Masu Kare Su Ba
Gwamnan ya ci gaba da cewa, “Ba za mu iya kwadaitar da siyasar rarrabuwar kawuna da adawa da ‘yan daba a jiharmu da muke kauna ba. Ina kira ga al’ummar jihar Nasarawa da su ga irin abubuwan da wannan gwamnati ta yi a fannin tsaro, da gyara tattalin arziki, samar da ayyukan yi da dai sauransu.
“Rantsuwar da na yi na yi wa jama’a hidima cikin himma, cikin tsanaki, da tsoron Allah, za ta ci gaba da zama ma’anar tsarin mulkinmu.”
A halin da ake ciki, Kakakin Majalisar dokokin jihar Nasarawa, Mista Ibrahim Balarabe-Abdullahi, ya bukaci gwamnatin tarayya da na Jiha da su kara kaimi a fannin tsaro da ilimi domin ci gaban al’umma gaba daya.
A cewarsa, babu wata al’umma da za ta samu ci gaba mai ma’ana ba tare da ingantaccen tsaro da ilimi ba.
Sai dai ya yabawa Marigayi Janar Sani Abacha, tsohon shugaban kasa, wanda ya amince da kirkiro jihar Nasarawa da iyayen jihar bisa kokarinsu na ganin jihar ta samu ci gaba.
Balarabe-Abdullahi ya kuma yi kira ga ‘yan siyasa da su mai da hankali kan yakin neman zabe da ya shafi al’amuran da suka shafi zaman lafiya da ci gaban kasa baki daya tare da samun nasarar zaben 2023 mai zuwa.
“Lokacin yakar kanmu ya wuce, yakinmu ya kamata ya dogara da abun da muke da shi.
“Ina kira ga matasa da kada su bari wani dan siyasa ya yi amfani da su. Ina so in yi kira ga matasa da su jawo hankalin ‘yan siyasa, masu son amfani da su wajen daba su yi amfani da ‘ya’yansu, su kuma ‘yan siyasa su kasance a sahun gaba,” inji shi.
A wani labarin kuma: Shugaban Jam’iyyar PDP Ya Dawo Najeriya Yayin Da Aka Fara Kamfen
Yayin da aka fara yakin neman zabe a hukumance gabanin babban zaben 2023, Shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Iyorchia Ayu, ya dawo Najeriya bayan tafiyar mako biyu da ya yi a Turai.
“Jirgin nasa ya sauka a filin jirgin saman Nnamdi Azikwe da ke Abuja, da misalin karfe 7 na na dare,” in ji mai ba Ayu shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Simon Imobo-Tswam, a wata sanarwa a ranar Juma’ar nan.