Jam’iyyar ADC reshen jihar Zamfara ta kammala zabukan fitar da gwani na jam’iyyar a jihar, inda ta tabbatar da cewa jam’iyyar za ta zama jam’iyya mai mulki a jihar a shekarar 2023.
Da yake jawabi ga magoya bayan jam’iyyar a Gusau, babban birnin jihar, shugaban jam’iyyar na jihar, Alhaji Kabiru Garba, ya bayyana cewa APC ta gaji kuma ba ta da cikakkiyar gogewar da za ta iya tafiyar da jihar Zamfara, inda ya ce jam’iyyar ADC za ta karbe jihar a 2023.
Shugaban ya ci gaba da cewa, matsalar rashin tsaro da tabarbarewar siyasa da ke addabar jihar za su isa al’ummar Zamfara su yiwa APC tawaye ta hanyar akwatin zabe a 2023.
KARANTA WANNAN LABARIN: 2023: Jam’iyyar APC Ta Fitar Da Cikakkun Jerin Sunayen ‘Yan Takarar Shugaban Kasa 13 Da Aka Tantance
Ina tabbatar wa al’ummar Zamfara cewa ADC za ta kawo sauye-sauye masu kyau a jihar da za su iya kawo sakamako mai amfani idan aka zabe su a 2023.”
Da yake jawabi a wajen zaben, shugaban kwamitin zaben wanda hedkwatar jam’iyyar ADC ta kasa ta aiko jihar Malami S. Galma ya yabawa wakilan da suka gudanar da zaben cikin lumana.
Ya kuma bayyana zaben a matsayin sahihi, karbabbe kuma mai cike da adalci, inda ya bukaci magoya bayan jam’iyyar ADC da su bada hadin kai domin samun nasarar jam’iyyar a zabe mai zuwa.
An zabi Jafar Salisu Gusau bisa hadin kai a matsayin mai rike da tutar jam’iyyar a jihar.
Sai dai kuma duk sauran mukaman da aka zaba su ma an yi su ne bisa yarjejeniya ban da mazabar Gusau/Tsafe ta tarayya inda ‘yan takara biyu Aliyu Sani Tsafe da Yusuf Sani suka fafata.
Sai dai Aliyu Sani Tsafe ya samu kuri’u 18 inda aka bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben yayin da abokin hamayyarsa, Alhaji Yusuf Sani ya samu kuri’u shida.
Comments 1