Tsohon shugaban kasa Goodluck Ebele Jonathan ya shawarci ‘yan Najeriya da su zabi shugabanni masu gaskiya wadanda suka sa kasar a zuciyarsu kuma za su dauki Najeriya a matsayin aikinsu.
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, Ya bayar da wannan shawarar ne a wata hira da manema labarai a Minna, jihar Neja ranar Alhamis din nan bayan ziyarar da suka kai wa tsohon shugaban kasa, Janar Abdusalam Abubakar, wanda ya dawo daga jinya a kasar waje.
Jonathan ya bukaci matasan kasar nan da su tabbatar sun zabi shugaban kasa wanda jama’a da kasarsa zasu ci muriyarsa.
Karanta kuma: Godluck Jonathan Ya Baiwa Matasa Wata Shawara Kan Zabe
Ya yi nuni da cewa, Janar Abduisalam Abubakar, wanda shi ne shugaban kwamitin zaman lafiya na kasa, dole ne ya fuskanci matsin lamba sosai gabanin zabukan 2023 domin tabbatar da gudanar da ayyuka cikin ‘yanci, gaskiya, da kuma lumana.
Tsohon shugaban kasar ya yaba da rawar da dattijon ya taka a zabukan kasar da ma yankin Afirka tare da yi masa addu’ar Allah ya ba shi lafiya.
Gidan talabijin na Channels ya rawaito cewa, Jonathan ya kuma kai ziyarar ban girma ga tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida a gidansa da ke Minna kafin ya koma zuwa Abuja.
A wani labarin kuma: Najeriya Ta Baiwa ‘Yan Kasashen Waje 286 Izinin Zama Dan Kasa
Gwamnatin tarayyar Najeriya ta bai wa ‘yan kasashen waje 286 da suka cancanci zama ‘yan kasa daga kasashe 49 da suka hada da Canada da Amurka da Birtaniya da kuma Girka izinin zama ‘yan Najeriya a wani biki da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranta a ranar Alhamis din nan a Abuja.
A jawabinsa a wajen taron bayar da kyautar da aka gudanar a dakin taro na Banquet Hall na fadar gwamnatin kasar, Buhari ya bayyana cewa amincewar ya yi daidai da tanade-tanaden kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya na shekarar 1999 (kamar yadda aka gyara) a babi na uku sashe na 26 da 27.