Tawagar diflomasiyya ta Amurka, Australia, Japan, Norway, Canada, da Burtaniya a Najeriya sun yi kira ga jami’ai da suka hada da hukumomin tabbatar da doka da oda da su tabbatar da yanayi mai kyau da kwanciyar hankali gabanin babban zabe.
Jaridar DIMOKURADIYYA ta tattaro cewa Tawagar diflomasiyyar ta yi wannan kiran ne a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Alhamis, inda ta bukaci hukumomin tsaro da su kasance cikin kulawa tare da mayar da martani daidai da duk wani lamari da ya shafi zabe.
“Muna kira ga jam’iyyu da su mutunta dokokin zabe da cibiyoyin zabe, su kuma dage wajen yakar tashe-tashen hankula da kalaman kyama daga magoya bayansu. Muna rokon jami’an tsaro a Najeriya da su yi iyakacin kokarinsu wajen kare wannan tsari da kuma dakile hare-haren da ake kai wa cibiyoyin INEC da kayan aiki da ma’aikata,” inji su.
Yayin da suke maraba da rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya ta biyu da ‘yan takarar jam’iyyun da zasu fafata a zaben shugaban kasa da ke tafe, jami’an diflomasiyyar suka ce sun jajirce wajen bayar da goyon baya ga duk wani kokari da zai tabbatar da cewa al’ummar Najeriya za su tantance wanda ya ci zabe.
Sun ce yana da matukar muhimmanci ga dorewar Najeriya da dunkulewar dimokuradiyya a gudanar da aikin kuma a kammala shi cikin aminci, cikin gaskiya, kuma cikin kwanciyar hankali.
Ofishin Jakadancin ya kuma ƙarfafa dukkan masu yin ruwa da tsaki da su sa baki cikin hanzari don kwantar da hankula da kuma guje wa duk wani tashin hankali a lokuta kafin, lokacin da kuma bayan zabuka.
Da suke kira ga dukkan jami’ai a matakin tarayya da na kananan hukumomi a Najeriya da su mutunta ‘yancin dan Adam da dimokuradiyya na ‘yan kasar, sun yi kakkausar suka ga ayyukan da ke kawo cikas ga gudanar da zaben cikin lumana da gaskiya.
Jaridar SOLACEBACE ta rawaito cewa Tawagar diflomasiyyar ta kuma bukaci dukkan ‘yan takarar shugaban kasa da jam’iyyun siyasa da su cika alkawuran da suka dauka a karkashin yarjejeniyar zaman lafiya ta biyu na amincewa da sakamakon zaben kamar yadda INEC ta sanar da kuma bin duk wani kalubale na sakamakon zaben ta hanyoyin da suka dace.
A Wani Labarin Kuma Ba Za Mu Rika Sanar Da Sakamakon Zabe Ta Intanet Ba — INEC
Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta Kasa (INEC) Farfesa Mahmood Yakubu ya fayyace cewa alkaluman sakamakon zabe ba za su rika yaduwa ta hanyar intanet din Hukumar ba.
Wannan na zuwa ne sa’o’i arba’in da takwas a gudanar da zabukan shugaban kasa da na ‘yan majalisar dokokin kasar.