2023: Osinbajo, Lawan, Amaechi sun ƙi halartar taron sulhun APC
Rashin halartar manyan ‘yan takarar shugaban kasa da suka fafata da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu, a ranar Larabar da ta gabata, ya kawo cikas ga taron sulhun da aka gudanar a Abuja.
KARANTA WANNAN LABARIN: Fadar Shugaban Kasa Ga Ortom: Ka Yi Ƙarya Akan Tsarin Tsaron Najeriya
Tinubu ya doke tsohon Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi; Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osibanjo da wasu mutane 12 domin samun tikitin takarar shugaban kasa na jam’iyyar.
Sai dai matashin dan takarar, Dakta Nicolas Felix, ya yi kira da a yi taro domin dinke baraka da kuma lalubo hanyoyin da za a bi domin ganin APC ta lashe zaben 2023.
‘Yan takarar shugaban kasa da aka gayyata taron sun hada da mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo; tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi; tsohon ministan kimiyya da fasaha, Ogbonnaya Onu; tsohon karamin ministan ilimi, Chukwuemeka Nwajiuba da tsohon ministan harkokin Neja Delta, Godswill Akpabio.
Haka kuma an gayyaci gwamnoni Yahaya Bello (Kogi), Dave Umahi (Ebonyi), Abubakar Badaru (Jigawa), Ben Ayade (Cross River) da Kayode Fayemi (Ekiti).
Sauran sun hada da shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan; tsohon gwamnan jihar Ogun kuma Sanata, Ibikunle Amosun; Sanata, Ajayi Boroffice; tsohon gwamnan Zamfara, Ahmad Sani Yerima; tsohon gwamnan jihar Imo, Sanata, Rochas Okorocha; tsohon shugaban majalisar dattawa, Ken Nnamani, tsohon kakakin majalisar wakilai, Dimeji Bankole; Fasto Tunde Bakare; Fasto kuma dan kasuwa, Dokta Nicolas Felix; tsohon ministan yada labarai, Ikeobasi Mokelu; Dan kasuwa, Tein Jack-Rich da mace daya tilo a cikinsu, Uju Ken-Ohanenye.
Sai dai wata sanarwa da mai kiran ya fitar, Dr. Nicolas Felix, ya sanar da dage taron yana mai cewa nan ba da jimawa ba za a sanar da sabon ranar.