Dan takarar gwamnan jihar Kaduna karkashin inuwar jam’iyyar APC Sanata Uba Sani ya ce taron da ya halarta na zaman lafiya wanda kwamishinan yan sanda na Kaduna Mista Yekini Ayoku ya shirya lamari ne mai matukar muhimmanci.
Wannan na cikin wata sanarwa da dan takarar na gwamna ya aikowa Dimokuradiyya a ranar Asabar din nan bayan kammala taron a ranar Juma’a.
KARANTA KUMA Burina Na Kai Jihar Kaduna Ga Kololuwar Nasarar Da El-rufa’i Ya Kai ta — Uba Sani
Sanata Uba Sani wanda shi ne sanatan Kaduna ta tsakiya mai ci ya ce “wannan taro cigaba ne wajen tabbatar da yakin neman zabe da zaben cikin lumana”
Ya ce “zabe ya zo kuma ya zama gasar da za a iya cewa mai rikici yayin da zaben yake gabatowa
“Amma yana da matukar muhimmanci a matsayinmu na yan takara, mu rika gargadar magoya bayanmu,” in shi.
Sanatan Kaduna ta tsakoyar ya yi kira ga magoya bayansa da su cigaba da nisantar kai hari da rikici domin gujewa tunzura jama’a.
Ya kuma bukace su da suyi watsi da yada labaran karya musamman a shafukan sada zumunta, ya kara da cewa su yi yakin neman zabe a shafuka da gudanar da ayyukan da doka ta tanada kamar yadda aka saba a bayan da yayin babban zaben 2023.
Duba kasa akwai wasu hotuna
A Wani Labarin Kuma Ku Daina farfaganda, Ku Mayar Da Hankali Kan Tsaro – PDP Ta Caccaki APC Zamfara
Shugaban riko na jam’iyyar PDP reshen jihar Zamfara Hon. Mukhtar Lugga ya koka da cewa ci gaba da cin zarafi da kame wasu masu ruwa da tsaki na jam’iyyar da jam’iyyar APC mai mulki ke yi ya sabawa doka kuma ya saba wa kundin tsarin mulki.
Lugga ya bayyana haka ne a lokacin da yake ganawa da manema labarai a Gusau babban birnin jihar, inda ya ce dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP a jihar, Dakta Dauda Lawal Dare yana da ‘yancin shiga jiharsa a duk lokacin da ya ga dama.