Tsohon gwamnan jihar Zamfara, Alhaji Abdulaziz Yari, da Sanata Kabiru Garba Marafa sun fice daga jam’iyyar APC mai mulki zuwa jam’iyyar adawa ta PDP.
Shugaban jam’iyyar adawa ta PDP a jihar, Kanar Bala Mande mai ritaya ne, ya bayyana hakan jim kadan bayan wani taron masu ruwa da tsaki a Gusau, babban birnin jihar, ranar Lahadi.
Kanal Bala Mande ya ce sun zauna sun kammala batun sauya shekar Yari da Marafa kuma sun cimma matsaya na yin aiki don ci gaban Jam’iyyar.
“Dukkanmu mun amince mu yi aiki domin ci gaban jam’iyyar, Kuma PDP a jihar ta yi musu maraba da zuwa ga jam’iyyar. Za mu tabbatar da adalci da ga dukkan membobin ko da mun ci zabe a 2023.
“Za a sanar da ranar da za a yi gagarumin liyafar tarban su a jam’iyyar mu daga baya amma za mu aiwatar da dukkan yarjejeniyoyin da aka cimma yayin taron masu ruwa da tsaki,” in ji Col. Mande.
Sakataren yada labarai na bangaren Yari na jam’iyyar APC, Alhaji Ibrahim Muhammad Birnin Magaji, ya tabbatar wa majiyar Jaridar Dimokuradiyya faruwar lamarin amma bai yi karin bayani ba.
“Eh, gaskiya mun koma jam’iyyar adawa ta PDP, kuma wannan shine abinda zan iya cewa yanzu,” in ji Birnin Magaji.
Yari da Marafa sun sha kaye a jam’iyyar APC a Zamfara bayan Gwamna Bello Matawalle ya sauya sheka zuwa jam’iyyar a bara.
Awani labarin kuma na daban.
Attajiri ya bada Kyautar coci mai kimar N60m ga al’umma a Kogi
Wani hamshakin dan kasuwa kuma mai taimakon al’umma a Jihar Kogi, Gabriel Enemona Onoja, ya bayar da gudunmawar coci mai kujeru 600 ga wata al’umma da ya zarga da yi masa rashin adalci.
Onoja ya ce duk da cewa mutanen sun taba neman ɓatar da shi ta hanyar magabatansa, amma ya yanke shawarar nuna soyayya ga al’ummar yankin.
Onoja, shugaban kuma wanda ya kafa gidauniyar Enemona-Josh Humanitarian Foundation, ya bayyana wannan karamcin a matsayin “wata babbar dama ta mayar da alheri da mugunta” ga al’ummar Inele-Ugog a Ƙaramar Hukumar Olaboro ta Kogi.
Da yake magana a lokacin kaddamar da cocin da aka baiwa United Evangelical Church, UEC, a jiya ko Asabar, Onoja, mai shekaru 37, ya ce ya manta da duk wani mummunan abin da ya faru a baya tsakaninsa da al’ummar.
“A matsayina na matashi, wanda yake fama da neman na abinci, ya jawo fushin dan uwana, wanda ya nemi rayuwata amma Allah ya taimake ni, na tsere, kuma yanzu Allah Ya albarkace ni.
“Ina matukar godiya ga Ubangiji da Ya ba ni damar kafa abinda zan dawwamar da kaina tun ina raye ta hanyar kammala wannan aikin cocin na Naira miliyan 60, wanda hakan abin kauna ne ga zuciyata da daukacin iyalina.
“Buri na shi ne duk wanda ya shiga wannan cocin, ya yi addu’a domin samun zaman lafiya, hadin kai, ci gaba da ci gaban tattalin arzikin Kogi da Nijeriya baki daya,” inji shi.