Kimanin malaman shari’a tara da manyan lauyoyi uku na Hukumar yaki da yi wa tattalin arzikin Kasa ta’annati (EFCC) na daga cikin lauyoyi 62 da aka bai wa matsayin babbar daraja ta manyan lauyoyin Najeriya (SAN).
DIMOKURADIYYA ta rawaito cewa, Kwamitin da ke kula da harkokin shari’a (LPPC) a karkashin jagorancin shugaban riko na babban jojin Najeriya CJN, Mai shari’a Olukayode Ariwoola ne ya karrama su da matsayin.
KARANTA KUMA: Masu Gabatar Da Kara Na EFCC Sun Sami Karin Girma Zuwa Matsayin SAN
Wata sanarwa da babbar magatakardar kotun koli, Hajo Sarki Bello ta fitar a yammacin ranar Alhamis din nan, ta nuna cewa LPPC ta ba lauyoyin mukamin ne a zamanta na 154 da ta gudanar a ranar 29 ga watan Satumba, 2022.
Jaridar Daily Post ta rawaito cewa, Malaman shari’a sun hada da Kathleen Ebelechukwu Okafor, Muhammed Taofeeq Abdulrasaq, Amokaye Oludayo Gabriel, Ismail Adeniyi Olatunbosun, Abdullahi Sheu Zuru, Joy Ngozi Ezeilo, da Theodore Bala Maiyaki,
Olaide Abass Gbadamosi da Chimezie Kingsley Okorie.
A wani labarin kuma: Najeriya Na Ci Gaba Da Jajircewa Wajen Hana Yaduwar Makaman Nukiliya – Buhari
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce Najeriya na ci gaba da jajircewa kan yarjejeniyar hana yaduwar makaman nukiliya.
yana mai cewa al’ummar kasar za ta ci gaba da inganta ta.
Buhari ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi ga wakilai a wani babban taro don tunawa da kuma inganta ranar yaki da makamin nukiliya ta duniya a birnin New York.