Ma’aikatar Ilimi ta Jihar Kano, a ranar Alhamis, ta amince da ranar 7 ga watan Afrilu, 2023, a matsayin ranar da za a fara hutun zango karatu na biyu/Ramadan ga dukkan makarantun gwamnati na furamare, sakandire na jeka ka dawo da na kwana da masu zaman kansu a fadin jihar, Punch ta rawaito.
Gwamnati ta bukaci iyaye da masu kula da daliban makarantun kwana da su kwashe ‘ya’yan su zuwa gida da sanyin safiyar Juma’a (gobe).
KARANTA WANNAN LABARIN: An Lakadawa Wani Mutum Da Ya Saci Kankana Dukan Tsiya Har Lahira
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Daraktan wayar da kan jama’a na ma’aikatar ilimi Aliyu Yusuf ya fitar.
A cewarsa, duk daliban da ke makarantun kwana za su koma makarantunsu a ranar 30 ga watan Afrilu, 2023, yayin da daliban da suke zuwa makarantun jeka ka dawo za su koma ranar 1 ga watan Mayu, 2023.
Ma’aikatar ta bukaci iyaye, masu kula da daliban, da daliban makarantun da su tabbatar da bin ka’ida, tare da amincewa da ranakun da za su ci gaba da aiki.
Ma’aikatar ta kuma yi wa daliban fatan samun nasara da hutun da babu matsala da kuma yin azumin Ramadan Kareem cikin amunci.
Sai dai kuma ta yi gargadin cewa za a dauki matakin ladabtarwa a kan daliban da suka gaza komawa makaranta a ranakun da aka bayyana.
A wani labarin kuma, Gwamnatin Legas Ta Rusa Wani Haramtaccen Gini
Hukumar kula da gine-gine ta jihar Legas ta ruguje wani gini wanda aka yi shi ta haramtacciyar hanya a karkashin wata hanyar wutar lantarki da ke kusa da titin Hamed Adebowale, Aguda a karamar hukumar Surulere ta jihar.
A cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar ranar Alhamis, Janar Manaja Gbolahan Oki, ya kawar da fargabar da ake da shi a kan ginin, inda ya kara da cewa, “Abun bala’i ne da ake jira ya afku saboda iskar da ake samu daga wutar lantarki, wanda hakan na iya haifar da tashin gobara.