Gamayyar jam’iyyun adawar kasar Kenya Azimio, sun bukaci a sake duba kundin tsarin mulkin kasar da aka shafe shekaru 13 ana yi, domin zama wani bangare a tattaunawar da suke yi da gwamnati domin kawo karshen zanga-zangar da ake yi a fadin kasar.
An bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da madugun ‘yan adawa Raila Odinga ya fitar, bayan wata ganawa da kungiyar ‘yan majalisar dokokin Azimio.
KARANTA WANNAN LABARIN: Peter Obi Ba Shi Da Wani Shiri Na Barin Najeriya – LP
A cewar BBC, sanarwar ta ce za su kara yin nazari a kan kundin tsarin mulkin kasar “don kawar da karshen shugabancin daular”.
‘Yan adawar sun yi nuni da “Cin nasarar-dukkan al’adun Kenya”.
A cikin watan Fabrairu, mataimakin shugaban kasar Rigathi Gachagua ya sha suka sosai saboda ya ce gwamnati tamkar kamfani ce mai hannun jari, wanda wasu ke da babban hannun jari, wasu kuma ko kadan.
Tuni dai ya kare kansa, inda ya ce yana magana ne kan nade-naden da gwamnati ke yi, wanda ya ce dole ne a raba tsakanin mutanen da ke goyon bayan ajandar shugaban kasa, ba dukiyar kasa ba, wanda ya ce za a raba daidai gwargwado.
Majiyar mu ta rawaito cewa Odinga yana gudanar da zanga-zangar mako-mako tun ranar 20 ga watan Maris na nuna adawa da tsadar rayuwa da kuma adawa da nadin sabuwar hukumar zabe ba tare da tuntuba ba.
Ya kuma sha tababa a kan sahihancin shugaba William Ruto, wanda aka zabe shi a bara, kuma kotun koli ta tabbatar da zabensa.
Akalla mutane uku ne suka mutu a zanga-zangar, an lalata wuraren kasuwanci da barnata kadarori masu zaman kansu musamman a manyan biranen Nairobi da Kisumu.
A ranar Lahadin da ta gabata ne shugaba Ruto ya bukaci babban abokin hamayyarsa a zaben bara, Odinga da ya dakatar da zanga-zangar da kuma ba da damar tattaunawa da majalisar dokokin kasar kan kafa sabuwar hukumar zabe, wanda Odinga ya amince da hakan.
Sai dai a ranar Talata shugaban ‘yan adawar ya kara da wata sabuwar bukatar tattaunawa ta waje da ta yi daidai da yarjejeniyar kasa ta shekarar 2008, wadda tsohon babban sakataren MDD Koffi Annan ya jagoranta bayan zaben shekara ta 2007 mai cike da takaddama.
Wasu shugabannin gwamnati sun yi kakkausar adawa da irin wannan mataki tare da zargin Mr Odinga da yunkurin yin kutsawa cikin gwamnati.
A shekarar 2007, yarjejeniyar ta kai ga kafa gwamnatin hadaka da shugaba Mwai Kibaki, inda Odinga ya zama Firaminista.
Odinga ya dage kan cewa ba ya son irin wannan tsari, amma tattaunawa ta gaskiya game da adalcin zabe tare da mafita ga karin zabuka na gaskiya.
Ya kuma sha alwashin komawa kan tituna domin gudanar da zanga-zanga idan har tattaunawar ta kasa yin tasiri.
Har yanzu dai kungiyar ‘yan majalissar dokokin kasar ba ta gabatar da kudurin nata na kin amincewa da shawarwarin ba, amma shugaban kasar ya bayyana karara cewa ba za a tattauna batun zabensa ba.
A wani labarin kuma, NNPP Ta Yi Watsi Da Sabbin Nade-Naden Da Gwamna Abdulrazaq Ya Yi
Jam’iyyar NNPP ta ce sabbin nade-naden maitaima na musamman guda uku da Gwamna AbdulRaman AbdulRazaq na jihar Kwara yayi ba membobinsu bane.
Shugaban jam’iyyar na jihar, Malam AbdulSalam AbdulRazaq ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a Ilorin ranar Alhamis.