Kotun Shari’ar Musulunci da ke zamanta a garin Kwana Hudu a ranar Juma’a ta yanke wa ma’aikacin Opay Rabi’u Isah Gaida hukuncin daurin watanni tara a gidan yari, Daily Post ta rawaito.
An gurfanar da shi a gaban kotun shari’ar ne bisa laifin zamba da kuma satar zabar kudi Naira dubu 300,000 mallakar wani Zubairu Murtala ta hanyar bankin yanar gizo.
KARANTA WANNAN LABARIN: Gwamnatin Kaduna Ta Sassauta Dokar Hana Fita Ta Sa’o’i 12 A Wasu Sassan Jihar
Dan sanda mai shigar da kara, Aliyu Abidin, ya shaida wa kotun cewa wanda ake zargin (Zubairu) ya yi korafin cewa wanda ake kara ya sace masa kudi Naira 300,000 ta hanyar yin musayar kudi ta yanar gizo ba tare da izininsa ba a lokacin da ya ba shi wayarsa ya bude masa asusun ajiyar kudi na Opay.
Wanda ake tuhumar ya amsa laifinsa bayan an karanta masa kunshin tuhume-tuhumen, inda ya ce ya yi amfani da kudin ne wajen yin caca ta BetNaija.
Alkalin kotun, Nura Yusuf Ahmad, ya yanke masa hukuncin daurin watanni uku bisa samunsa da laifin cin amana da kuma wata shida saboda sata, sannan ya umarce shi da ya mayar da kudaden da ya sata na Naira dubu N300,000.
A wani labarin kuma, An Yankewa Wata Uwa Hukuncin Daurin Rai Da Rai Bisa Lakadawa Diyarta Dukan Tsiya Har Lahira
An yanke wa wata uwa a Houston hukuncin daurin rai da rai a gidan yari saboda ta yiwa diyarta dukan tsiya har lahira, in ji lauyan gundumar Harris Kim Ogg.
An yanke wa Tradezsha Trenay Bibbs, mai shekaru 29, hukuncin daurin rai da rai a ranar Litinin, 3 ga watan Afrilu, bayan da aka same ta da laifin kisan kai kan mutuwar Brielle Robinson mai watanni 4 a ranar 16 ga watan Afrilun shekarar 2016.