Babban Lauyan Tarayya AGF kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami, SAN, ya yi alhinin rasuwar tsohon babban Lauyan Tarayya kuma Ministan Shari’a a tsakanin shekarar (1985-1991) Prince Bola Ajibola SAN.
Malami ya ce rasuwar marigayi Bola Ajibola ya haifar da wani babban gibi a fagen shari’ar kasar, inda ya kara da cewa a matsayinsa na dan kasa mai kishin kasa, marigayi tsohon babban lauyan gwamnatin tarayya kwararre ne a fannin shari’a da ya shahara a duniya wanda tasirinsa ya kasance ba za’a iya mantawa da shi a tarihin Najeriya da ma bayansa ba.
KARANTA WANNAN LABARIN: Dalilin Da Yasa Atiku Ya Fadi Zaben Shugaban Kasa – Sanata Obinna Ogba
Yayin da yake addu’ar Allah ya jikan marigayin, Malami ya kuma yi addu’ar Allah ya baiwa iyalan marigayi tsohon AGF jihar Ogun da ma daukacin al’ummar kasar baki daya hakurin jure rashin da ba za a iya kwatantawa dashi ba.
Sakon ta’aziyyar Malami a cikin wata sanarwa da mai taimaka masa na musamman kan harkokin yada labarai da hulda da jama’a, Dakta Umar Jibrilu Gwandu ya fitar, ya roki Allah Madaukakin Sarki da Ya baiwa Ajibola Jannatul Firdaus.
A wani labarin kuma, Kidayar 2023: NPC Ta Horar Da Ma’aikata 5,000 A Jihar Adamawa
Hukumar kula da kidayar jama’a ta kasa NPC, za ta horas da ma’aikata 5,000 domin gudanar da kidayar jama’a da gidaje ta shekarar 2023 a jihar Adamawa.
Ma’aikatan sun hada da ma’aikata na dindindin da kuma ma’aikatan wucin gadi don yin atisayen a kananan hukumomi 21 na jihar.