Daga: Muhammad Gambo Damaturu
- Hukumar kidaya ta kasa, rashen Jihar Yobe ta bayyana dalilan dage lokacin kidaya.
- Kwamishinan Tarayya na Hukumar mai kula da reshen jihar Yobe Alhaji Mai Aliyu Muhammad ne ya bayyana dalilan da suka sa aka dage kidayar.
- NPC tace hukumar ta samu kalubale na rashin kudaden gudanar da aikin.
Idan za a iya tunawa, makwanni kadan da suka gabata, hukumar kidaya ta kasa (NPC) ta sanar da cewa an dage lokacin yin kdayar.
Tun lokacin dai, a jihar Yobe, babu wata tattaunawa da ta gabata tsakanin hukumar da manema labarai.
KARANTA WANNAN: An Sanya Ranar Da Za’a Gudanar da Babban Zaben Wata Kasa a Afirka
Kwamishinan Tarayya na Hukumar mai kula da reshen jihar Yobe Alhaji Mai Aliyu Muhammad a ranar 31 ga watan Mayu ya shirya taron manema labarai inda ya bayyana musu dalilan da suka sa aka dage kidayar.
Yayin da yake cewa “hukumar ta kammala dukkan wasu shirye-shirye, yace hukumar ta samu kalubale na rashin kudaden gudanar da aikin.
Mai Aliyu ya kara da cewa hukumar ta bukaci kudi kimanin Naira Biliyan 327.2 don yin ayyukan da suka hada da horar da masu aikin tattara bayanai da sauran su, inda yace Gwamnatin Najeriya ta saka kaso 46 daga cikin abun da hukumar ta nema.
Yace yanzu haka, akwai gibin kudaden wanda adadin su ya kai Naira Biliyan 176.7.
JARIDAR DIMOKURADIYYA ta rawaito cewa hukumar ta so ta kammala kidayar kuma ta bayyana sakamako kafin sabuwar Gwamnati ta karbi mulkin kasar sai dai hakan bai samu ba.
Daga bisani yayi godiya ga dukkan abokan hulda da suke taimakawa hukumar wajen isar da ayyukan ta.
A wani labarin kuma, Ka Cika Alkawuran Yakin Neman Zaben Daka Dauka, dan Takarar Gwamnan AAC ga Mbah
Dan takarar gwamna a jam’iyyar African Action Congress, AAC, a zaben da aka yi a ranar 18 ga watan Maris a jihar Enugu, Ray Kene Ogbodo, ya tuhumi sabon gwamnan jihar Enugu, Barista Peter Mbah da ya cika alkawuran yakin neman zabensa kamar yadda yake kunshe a cikin littafinsa.
Ogbodo ya yi wannan tuhumar ne sa’o’i 48 bayan bikin rantsar da Barista Mbah da mataimakinsa, Barista Ifeanyi Ossai a Dandalin Michael Okpara dake Enugu.