- Gwamnatin Kano ta yi nasarar kwashe fiye da tireloli 400 na sharar gida a cikin kwanaki uku da fara gudanar da aikin.
- Daukar matakin shine don tabbatar da yadda ake zubar da shara a manyan titunan da kuma hana toshe magudanan ruwa.
- Hakan zai kawar afkuwar ambaliyar ruwa, musamman a yanzu da muke cikin lokacin damina.
Kwamitin hadin gwiwa mai yaki da kwashe shara a birnin Kano, a ranar Alhamis, ya tabbatar da cewa ya yi nasarar kwashe fiye da tireloli 400 na sharar gida a cikin kwanaki uku da fara gudanar da aikin,Punch ta rawaito.
Babban Sakataren Ma’aikatar Muhalli, Alhaji Aliyu Yakubu Garo (Turakin Garo) ne ya bayyana haka a ranar Alhamis yayin ziyarar duba da kuma sa ido kan aikin kwashe shara a cikin birnin Kano.
KARANTA WANNAN: An Shiga Rudani Ya Yin Da DSS Sukayi Yunkurin Cafke Zababben Dan Majalisa
Idan dai ba a manta ba jam’iyyar NNPP mai ci ne ta jagoranci gwamnatin Injiniya Abba Kabir Yusuf ya kafa kwamitin hadin gwiwa, kan batun kwashe shara a cikin birnin Kano.
Kwamitin yana karkashin jagorancin Ambasada Ahmadu Haruna Danzago, yayin da babban sakataren ma’aikatar muhalli shi ne sakataren kwamitin, tare da sauran mambobin da aka dorawa alhakin kwashe shara a cikin babban birnin Kano.
Makasudin wannan atisayen dai shi ne tabbatar da yadda ake zubar da shara a manyan titunan mu da kuma tabbatar da tsaftar Kano, ba ta da shara da kuma hana toshe magudanan ruwa, domin kare afkuwar ambaliyar ruwa, musamman a yanzu da muke cikin lokacin damina.
Babban Sakataren ya ziyarci wurare kusan 20 a cikin birnin Kano, inda ake ci gaba da gudanar da aikin, ya kuma yaba wa jama’a bisa hadin kai da goyon bayan da suke bayarwa wajen ganin an samu nasarar kwashe sharar.
Har ila yau, ya bukaci mazauna yankin da su yi koyi da al’adar kawar da magudanar ruwa a kai a kai, don gujewa ambaliya.
Ya yaba da irin yadda wasu masu hannu da shuni ciki har da shugaban kungiyar Alhaji Ahmadu Danzago da sauransu suka yi na ganin an gudanar da wannan aiki cikin kwanciyar hankali, wanda abin a yaba ne matuka.
Garo ya kuma yi nuni da cewa, gwamnatin Engr. Abba Kabir Yusuf a cikin kankanin lokaci da hawan kujerar shugabancin sa ya nuna sha’awarsa da kuma himma wajen kare rayuka ta hanyar inganta tsaftar muhalli, da kuma umarninsa ga mazauna Kano na yin amfani da kwanduna wajen zubar da shara, da dai sauransu.
Da yake tsokaci kan yadda ake gudanar da aikin kwashe sharar a cikin birnin Kano, babban sakataren ya bayyana fatan cewa idan har aka dore da wannan dabara, Kano za ta sa sabon salo.
Da yake jawabi a madadin jama’ar yankin Kurna Asabe da ke karamar hukumar Dala, Mallan Usman Nuhu ya yaba wa Gwamna Kabir Yusuf bisa wannan shiri na tsaftar da ya fito da shi, wanda ya bayyana a matsayin wanda ya dace a shekarar 2022 cewa sharar da aka kwashe tsawon wata guda ana tarawa a yankin.
“Hakan ya haifar musu da ƙalubale mai tsanani da kuma fallasa rayuwarsu ga haɗarin muhalli.
A wani labarin kuma,Gwamnatin Zamfara ta yi gargadi kan sanya alluna masu dauke da hotunan Gwamna
Gwamnatin jihar Zamfara ta yi gargadi kan sake bullowa tare da nuna baje kolin alluna masu dauke da hotunan gwamna Dauda Lawal a babban birnin jihar da kuma kananan hukumomin jihar ba bisa ka’ida ba.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwar manema labarai da Mustapha Jafaru Kaura babban mataimaki na musamman ga gwamnan jihar kan harkokin yada labarai ya raba wa manema labarai a Gusau babban birnin jihar.