Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta sanar da Mista Abdulkarim Chukkol a matsayin mukaddashin shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa,Punch ta rawaito.
Wannan na zuwa ne sa’o’i 24 bayan shugaban kasa, Bola Tinubu, ya dakatar da tsohon shugaban hukumar, Mista Abdulrasheed Bawa.
KARANTA WANNAN: Da Dumi-Duminsa: EFCC ta samu mukaddashin shugaban hukumar
Ga Abubuwa Biyar Da Ya Kamata Ku Sani Game Da Sabon Shugaban EFCC.
1. Chukkol tsohon dalibi ne a Cibiyar Bincike ta Tarayya da ke Quantico, Cibiyar Nazarin Tsaro ta Turai da ke Jamus, sannan kuma ya halarci makarantar War College dake Najeriya.
2. Ya yi digirin farko a fannin tattalin arzikin noma daga Jami’ar Maiduguri a shekarar 2000 da kuma Post Graduate Certificate a Criminal Justice Education dake Jami’ar Virginia ta Amurka.
Haka kuma ya yi Diploma a fannin tsaro na Intanet da Spectrum Management daga Hukumar Sadarwa ta Amurka. Cibiyar Horarwa dake Washington DC, Amurka.
3. Kafin sabon mukamin na sa, ya kasance Daraktan ayyuka na hukumar EFCC.
4. Mutum ne na farko a hukumar kuma fitaccen memba a EFCC Cadet Course One. Ya taba rike mukamin Shugaban Sashen Zamba da Laifukan Intanet na shiyar Legas da Abuja tsakanin shekarun 2011 zuwa 2016.
Sannan ya kasance tsohon kwamandan shiyyar Uyo a shekarar 2017 da kwamandan shiyyar Fatakwal a shekarar 2020.
5. Ya lashe kyautuka da yabo da yawa a cikin gida da waje, ciki har da “Kyauta mafi kyawun aiki” da EFCC ta bayar da kuma “Kwazon Kwarewa” da Ma’aikatar Shari’a ta Amurka ta bayar, da dai sauransu.
A wani labarin kuma, Tinubu yana gana wa da Abdulsalami Abubakar a fadar gwamnati
A halin yanzu dai shugaba Bola Tinubu yana ganawa da tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Janar Abdulsalami Abubakar (mai ritaya), a fadar shugaban kasa dake Abuja.
Abubakar wanda kwanan nan ya cika shekara 81 a duniya ya ziyarci Tinubu sa’o’i 48 bayan tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya je fadar Villa domin yi wa shugaban kasa bayanin abubuwan da ke faruwa a Mali.