Ma’aikatar lafiya ta tarayya ta gargadi maniyyatan Najeriya da suka je aikin hajjin bana a kasar Saudiyya da su guji cin ganda, naman da ka turara da hayaki da kuma naman jeji a kasa mai tsarki biyo bayan bullar cutar anthrax, cutar zoonotic da ta fi shafar dabbobi da mutane a wasu kasashen dake makwabtaka da Najeriya,Tribune Online ta rawaito.
Wannan gargadin yana kunshe ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Kwamishinan Lafiya, Hukumar Hajji ta Kasa (NAHCON)/Ma’aikatar Lafiya ta Tarayya, Dr Saidu Ahmed Dumbulwa.
KARANTA WANNAN: Sojojin Sudan Sun Zargi RSF Da Alhakin Mutuwar Gwamnan Darfur Ta Yamma
Shawarar wacce aka ba da umarni ga daukacin tawagar likitocin NAHCON da ma’aikata da kuma mahajjata, ta yi nuni da cewa ma’aikatar noma ta tarayya ta sanar da ma’aikatar lafiya ta tarayya game da bullar cutar a wasu kasashen da ke makwabtaka da yankin yammacin Afirka. musamman Ghana, Burkina Faso da kuma Togo.
Ya ce: “Ana samun ƙwayar cutar Anthrax a cikin ƙasa kuma yawanci tana cutar da dabbobin gida da na daji.
“Ba masu yaduwa ba ne, amma mutum na iya kamuwa da cutar ta hanyar mu’amulla da dabba mai cutar ko gurbataccen kayan dabbobin.
“Cutar tana da alamun mura kamar tari, zazzabi da ciwon tsoka. Idan ba iya gano cutar ba kuma an yi maganinta da wuri, zai iya haifar da matsanancin ciwon huhu, wahalar numfashi, firgita da mutuwa.
“Duk da haka, kasancewar kwayar cuta, yana amsa maganin rigakafi.
“Da farko cutar dabba ce. Dabbobin da ba a yi musu allurar rigakafin cutar anthrax ba suna iya yaɗata ga mutabe cikin sauƙi ta hanyar shakar daɗaɗɗen anthrax ko kuma shan kayan da ake amfani da su na anthrax kamar fata da ganda, nama da madara.
“Don haka, Ma’aikatar Lafiya ta Tarayya ta yi niyyar ba da shawarar cewa maniyyata a kasar Saudi Arabiya da su daina cin naman ganda,naman da aka babbaka da hayaki, naman daji har sai an shawo kan lamarin saboda suna haifar da babbar hadari ga alhazai”.
Dokta Dumbulwa ya nuna damuwarsa kan yadda mahajjata da ‘yan kasuwa daga jihohin kudu maso yammacin kasar da ke kan iyaka da Jamhuriyar Togo za su iya fitar da irin wadannan kayayyakin dabbobi zuwa kasashen waje.
Ya bukaci dukkan ma’aikatan kungiyar likitocin NAHCON da su “lura kuma su ba da shawarar yadda ya kamata a matsayin matakan kariya.”
A wani labarin kuma, Har Yanzu Peter Obi Ne Dan Takarar Da Najeriya Ta Fi Bukata – Obasanjo
Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo, ya ce dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour a zaben shugaban kasa da za a yi a ranar 25 ga watan Fabrairu, Peter Obi, shi ne dan takarar da ya dace ga Najeriya.
DAILY POST ta ruwaito cewa, Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, ta bayyana dan takarar jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki a wancan lokaci kuma shugaban kasa, Bola Tinubu, a matsayin wanda ya lashe zaben.